Takaitaccen Tarihin Masana'antar Kannywood da Babban Jagoran ta

Kannywood masana’antar shirin hausace ta cikin gida da mazauninta ke Jahar kanon Nijeriya, sunan dai wani jagorane ya lakaba mata shi a shekarar 1990. To kenan kunga ta girmi takwararta Nollywood. Ba wanda zai yi bayani game da kannywood ba tare da ya ambato sarkinta ba- cewa da sarkin kannywood, wanda bai wuce kowa ba sai Ali Nuhu.

Ali Nuhu ɗa ne ga wani tsohon Ɗan siyasa a Nijeriya, Nuhu Poloma ɗan Jahar Gombe, amman shi ya taso a Jahar ta Kano. Ya samu B.Sc ɗi tai a ilmin kimiyar yanayin ƙassai (Geography) a Jami’ar Jos ya kuma yi bautar ƙasa a Ibadan, Jahar Oyo. Kafin nan, ya fara shiri a Jami’ar ta Jos. Ya ƙara da cewa ya kan kalli shirin kwaikwayon wanki da wanke-wanke (soap operas) kuma wannan ya ƙara bashi ƙwarin guiwa. Wannan ne ya bashi wani ɗan ɓangaren ga shirin; kuma ɓangaren ne sanadiyar ɗagawatai zuwa yanzu.

Ya kasance tun shekarun, wani gimshiƙi ga masana’antar kannywood da kuma gwani ga yawancin ƴan wasan kwaikwayon na yanzu, har da gwarzon mai bada umarni, ɗan wasan kwaikwayon nan Adam A Zango, Zainab Indomie, Gwarzon jarumi mai tasowa Nuhu Abdullahi da wasu.

Ali Nuhu uba ne ga ɗiya ukku, a kannywood ana mai laƙabi da “Sarki”, ya fito ga ɗaruruwa shirin gida kannywood da kuma wasu na turanci a masana’antar Nollywood, kuma tun nan yake samun magoya baya da karamomi daga magoya bayanai. Nuhu na samun bibiya a Afruka da wajen Nijeriya gaba ɗaya. Maganar yawan magoya baya da abun hannu kuma, ya kasance ɗaya daga jigajigan ƴan wasar kwaikwayo a Afruka.

Miliyoyin magoya bayan Ali sun san shi matsayin ɗan wasa mai ƙwazo wajen bada umarni da kuma wanda ya samu karamomi da dama kasancewatai mai shiri, bada umarni, rubuta labari da kuma taka rawa a yawancin ingantattun shirin na kwaikwayo. Amman yanzu ya dakatarda duk waɗannan zuwa jami’ar shirinkwaikwayo, University of Southern California School of Cinematic Arts, USA dan ƙaro ilimi.

Abdul Mailahiya Hausa

I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder and Operator at Bago Technologies. My hobbies are Reading, Travelling and Discovering.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post