Abubuwan ban Mamaki 15 da ba ku sani ba gameda Rakumai

Wasu mutane na yawan danganka Rakumai da hamadar Gabas ta tsakkiya, duk da cewa akwai miliyoyin waɗannan bisashen masu tozo a yankin Afrika. Ana samun yawancinsu a Kasashen Afrika – cikin Masar da Moroko dakeda iyaka da Hamadar Sahara; ko cikin Kasashen Afrika da ake kira da Kahon Afrika “Horn of Africa” kamar Ethiopia da Djibouti d.s.s. Cikin Yankin Afrika ta yamma kuma ana samunsu a ƙasashe irinsun Jamhoriyar Nijar, Mali da Nijeriya.

Akwai ire-iren Rakumai kashi biyu;
Rakuman Dromedary ko Rakuman Larabawa: Waɗannan sune masu tozo guda da Rakuman Bactrian masu tozaye guda biyu. Waɗannan ire-iren Rakuman gida biyu ana samunsu a yankuna dabam-dabam a faɗin duniya.

Rakuman Dromedary: Ana kiransu kuma da Rakuman Larabawa, su ana samunsu a Arewaci, Yammaci da Gabas ta tsakkiya, wadannan irin tozo guda kaɗai ke garesu.
Rakuman Bactrian: Waɗannan ana samunsu a yankin Asiya ta tsakkiya, waɗannan sun sha bam-bam da na farkon; sune Rakumai masu tozo guda biyu, sunada yawancin gashi a jikinsu saboda yanayin mazamninsu kuma an fi amfani dasu ga ci da sarrafa gashinsu in aka keɓe na farkon. Ba tareda bambantawa ba, Rakumai ana samunsu a hamada. Amman mutane na ganin cewa Rakumai na zama ne a wurare masu yanayin zafi, suna yi a kasashen masu yamyin sanyi. To ga jerin “Abubuwan ban mamaki 15 da baku sani ba gameda Rakumai.”

 1. Raƙumai nada kaifin ƙwaƙwalwa sosai fiyeda kowace dabba a duniyar dabbobi. Sunada yawan tunani kuma suna tunowa da komi. Idan mutum ya ɓatama Raƙumi rai ba zai taɓa mancewa ba kuma zai yi duk mai yuwuwa ya ga ya kama mutum. Kuma in rana ta ɓace, in ba’a yi sa’a ba, zai iya kashe mutumin. Sunada ganewa, suna ƙyale yara ƙanana idan sunka taƙulesu, amman sukan gwammace ramawa idan manyane dan suna ɗaukar abun kamar reni.

 2. Rakumai dabbobine masu kyautata zamantakewa tsakaninsu, suna yin gungu-gungu da babban jagoransu Amale, inda kuma ƙananan Rakumai ke nasu gungu na dabam da ake kira “Bachelor herd” a turance. Rakumai na kyautata zamntakewa matuƙa kuma suna gaisuwa tsakaninsu ta hanyar hurji ga fuskoki yanuwansu.

 3. Rakumai na iya gudun da yakkai nisan kilo 40 cikin sa’i guda sanda ubangidajensu ke cikin sauri ko a’a.

 4. Ana alaƙanta Rakumai da cewar baiwa daga Allah dan saboda rawar da sunka taka a da lokacin daure da aka sha yake-yake.

 5. An san Rakumai da tofama mutane miyau. A gaskiya, suna fitarda abuncin dake cikin cikinsu tareda miya ɗin. Wannan hanyar kariyace in aka ɓata masu rai.

 6. Rakumai nada jerin gira biyu masu kabrin gaske dake kare idanuwansu daga ƙurar Hamada. Suna kuma iya daɗe hantunansu da laɓɓansu dan fitarda ƙurar.

 7. Rakumai na iya cin kusan komi mai ciyuwa ba tareda sun jima bakunansu ba, harda ƙayoyi da ƙaimu. Bisashene masu cin haki, kenan, ba zaku taɓa ganinsu suna cin nama ba.

 8. Fitsarin Rakumai kabri gareshi kamar madara dan suna adana ruwa. Da kashinsu da fitsarinsu duk ana amfani dashi wajen magani.

 9. Nononsu wanda yakeda ƙamshin itatuwa, yanada amfani ga lafiyar jikin mutane, yana tattareda yawancin sinadarin dake tabbatarda lafiyar jiki, kyawon jiki, kuma yanada ƙaramcin kitse. Yana taimakawa wajen kare lafiyar jikin mutum, tabbatarda gudanar jini, tabbatarda girma ga kananan yara, maganin cutar zaki (diabitis) d.s.s

 10. Tozon Rakumi ba ma’adanar ruwa bace kamar yanda mutane ke zato. Duk da cewa suna zama a wurare masu yanayin zafi, tozonsu na adana kitse kuma yana taimakama jikinsu ya sanyaya. In suna bukata, kitsen na zamewa abunci da ruwa dan amfani garesu.

 11. In Rakumi ya kusanta ga ruwa, yana shan ruwa da sauri, yakan sha adadin da yakkai jarka 30 cikin mintuna 13. Jikin Rakumi na shan ruwa fiyeda na kowace dabba a doron kasa.

 12. Uwa Rakuma na ɗaukar cikin Jaririn Rakumi tsawon kimanin watanni sha-hudu (14) kamin ta haihu.

 13. Bayan waɗannan abubuwan ban mamaki da ban al’ajabi da Allah ya huwacema Rakumaj dashi, Ubangiji cikin nashi iko na dabam ya ƙaddaro masu tsoron Kunama. Da hango ƙanƙanuwar Kunama daga nesa, Makeken Rakumi zai nemi hanyar mafita dan harbin kunawa garesu tamkar mutuwa ce dan takunansu tabshi garesu kamar kaɗa.

 14. Rakumai bisashe ne wanda aka sha jigila dasu a Hamadar Sahara tsawon zamani: Misali da Abzinawan Agadez a Jamhoriyar Nijar.

 15. Da ƙarshe, A cikin Alkur’ani mai tsarki an ambaci halittarsu mai ban mamaki a wata aya, “Basu ga Rakumai ba, yanda aka haliccesu?― Da kuma sararin samaniya, yanda aka ɗagata sama? Da tsaunukka yanda aka kakkafasu?― Da doron kasa, yanda aka shimfidata?”
  (al-Ghashiya, 17-20)

Abdul Mailahiya Hausa

I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder and Operator at Bago Technologies. My hobbies are Reading, Travelling and Discovering.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post