Abubuwan morewa 11 tattareda Ɗiyan itace da Kayan Ɗanyen da mu ke ci kullum

Kusan kowanenmu mun ɗauki tabi’ar cin Ɗiyan itatuwa da kayan ɗanye a ko da yaushe. Dukda haka, sun zame muna ɗaya daga cikin abuncinmu tun zamani mai tsawo. Muna cinsu ɗanyu, da sanyi, shan ruwansu kuma muna haɗawa da kowane irin abuncin da muke ci. Amman kaman waɗansu abubuwan da sunka daɗe, akwai bayanan ɓoye da baku sani ba wanda sukeda ban mamaki tattare dasu da ya kamaceku da sani.

Majiyar (IslamCan.com) ta kasance kafar da na fi so tun sanda na fara shiga yanar gizo. Wannan kaface da nake dibawa duk sanda naji zan karanto koyarwa ta tafarkin musulumci da sauransu. Makarantace mai zurfi da ta tanadi bayanai da dama dan kowane musulmi da ma wanda ba musulmi ba.

Waɗanan sune bayanan na Kimiya 11 gameda ɗiyan itatuwa da kayan ɗanyen da muke ci kusan kullum:

Karat:
Cikin yankakken karat na kama da ƙwayan idon mutum. Ƙwayar, ɗanɗashen da shayukkan nada kama da na idanun mutum…kuma hakane, kimiyan yanzu ta gano karat na ƙwaran da gaske wajen tabbatarta gudanan jini ga idanuwa.

Tummati:
Rababben tummati nada makamai huɗu kuma ja-ja wur. Zucciya ja ce kuma tanada makamai huɗu. Dukan binciken yau ya gano cewa tummati na daga abuncin zucciya da jini.

Inabi:
Ɗiyan inabi sarkahe suke da kama irin ta zucciya. Kowane ɗan inabi nada kaman ɗigon jini kuma bincike yau ya nuna cewa inabi shima abuncin zucciya da jini ne.

Gujjiyar wal:
Gujjiyar wal nada kama da ƙaramar ƙwaƙwalwa, rabin ƙwalo na hagum da kuma na dama, ƙwallon bisa da ƙasa. Harda tamoji ko dunƙule ke akwai ga ɗan gujjiyar tamkar ɗan ɓawo. Yanzu mun gano cewan gujjiyar wal na taimakawa wajen gamsarda tari 3 wajen watsa sinadarin wasa ƙwaƙwalwa.

Wake:
Wake na magani da kuma dadaita lafiyar ƙwadan mutum kuma hakane, wake nada kama da ƙwadan ta mutane.


Gangamau:
Iccen gangamau, alayyahu da dangi nada kama da ƙashi. Wannan abuncin na kiyaye ƙarfin ƙassa. Ƙassa sun tanadi sinadarin sodium kashi 23 kuma waɗannan kayan ɗanyen su ma sun tanadi kashi 23 na sinadarin na sodium. In babu cikakken sinadarin sodium a abuncinku, gangan jiki na janyoshi daga ƙassai, wanda ke sa su raunana. Wannan abuncin na maye gurbin sinadaranda ƙassai ke buƙata ga jikin mutum.


Gauta, Yalo da Dan Avocado na tabbatarda lafiya da kiyaye ciki da mahaifar macce – suna kama da waɗannan gaɓɓai. Bincike a yau ya gano cewa in macce ta ci dan Avocado guda a sati, yana daidaita kwayoyin hormones, kiyaye girman jariri kafin haihuwa da kare ciwon dajin mahaifa. Da mi wannan yayi kama? …. Yana ɗaukan daidai watanni 9 ga Dan Avocado ya girma tun daga hure zuwa nuna. Akwai sinadarai fiyeda 14,000 tattareda ɗayan wannan ɗan itaciyar (kimiyar zamani ta karanto da gano 141 kaɗai daga cikinsu).

Ɗiyan Baure cike suke da ɗiya kuma sarkahe su guda biyu sanda suke girma ga uwar icce. Ɓure na ƙara ƙarfin maniyin namiji da kuma ƙara yawan ƙwayoyin maniyin da kare rashin mazakutar namiji.

Grapefruits, Lemu, da dangin ɗiyan itatuwa na tamkar kama da hantsar nonon macce kuma suna tabbatarda lafiyar gudanan ruwan nono daga ciki da waje nonuwa.

Albasa na kama da ɗigon ruwan jiki. Binciken yau ya gano cewa Albasa na share dauɗa daga ruwan jiki. Tana kuma haifarda hawaye wanda ke wanke wajen idanuwa.

Dankali na kama da gaɓa wadda ke daidaita tace da narke abunci kuma yana tabbatarda ƙayyade ciwon sukari.

Inabi na taimaka lafiyar da aikin marenan macce dake cikin ciki. To kenan wane falalolin Ubangijinku zaku guje? – [Alkur’an 55:13]

Abdul Mailahiya Hausa

I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder and Operator at Bago Technologies. My hobbies are Reading, Travelling and Discovering.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post