Ɗan Tahalikin nan Buhari ya rasu – Wanda kishiya ta yanke Mazakutar shi

Karamin Jariri Dauda Buhari, wanda kishiyar uwa, Bara’atu Rabi’u ta yankema mazakuta, da bisani Allah ya mai rasuwa bayan yar rashin lafiya ran Laraba.

Babbar shugaba mai kula da karen hakkin yara kanana, Mariam Kolo, ta bayyana cewa Buhari ya mutu a Kauyen Wada dake karamar hukumar Shiroro a Jahar Niger, bayan zazzabin cizon sabro.

Yayin magana da Punch, ran Laraba, Kolo tacce, “Buhari yayi fama da dan zazzabi wanda yanayinshi yayi sama kuma ya mutu tun kafin ma a bashi magani.”

Kolo ta bayyana cewa Buhari ya mutu a lokaci sanda aka kayyade yi mai dashen mazakuta a United Kingdom, UK.

DG din tacce rashin lafiyar bata da alaka da ciwon da ya ji dag ta’adi, dan yana cikin koshin lafiya biyo bayan ayukkan fidar da aka mai.

Nuna bakin cikin mutuwar jaron wanda yanzu yake cikin shekaru biyu da haihuwa, Kolo tacce shari’ar kishiyar uwar wadda yanzu take tsare a gidan kaso, Old Minna Prison zata harraka.

In ba’a mance ba, kishiyar uwar Buhari, Bara’atu Rabiu, a watan Yuli 18, 2016, ta yankema jaririn mazakuta tun yana dan watanni biyu da haihuwa.

Bara’atu wadda a lokacin take cikin shekaru 17, bata bada dalilin aikata wannan mugun aiki ba.

Abdul Mailahiya Hausa

I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder and Operator at Bago Technologies. My hobbies are Reading, Travelling and Discovering.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post