An Tsaida Ranar Dawowar Shugaba Muhammadu Buhari

Muhammadu Buhari, Shugaban Nijeriya wanda ya je kasar United Kingdom dan kula da lafiyarshi tun 7 ga watan Mayu 2017 yanzu ance yana nan yana shirye-shiryen dawowa kasar.

Labari dangane da dawowar shugaban ya zo tun kafin wani hoton farko da ya watsu a yanar gizo.

Fadar shugaban kasa ta musa sahihancin hoton wanda wani dan kungiyar Muryar Afruka ya watsa “Voice of Africa”, tacce bai da tushe kuma a dauke shi haka.

Ta bakin Sahara Reporters, Shugaban Nijeriyar na shirin komowa Kasar daga United Kingdom ran 27 ga watan Yuli 2017.

Labarin ya zo biyo bayan sharri da Gwamnan Jahar Ekiti, Ayodele Fayose yayi baya-bayan nan inda yake cewa mutanen dake karkashin Shugabancin Buhari na ganin zasu dawoda shugaban a kasar dukda ciwon nashi yaki ci yaki canyewa.

Abdul Mailahiya Hausa

I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder and Operator at Bago Technologies. My hobbies are Reading, Travelling and Discovering.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post