Bikin Noman Gayya: Abubuwan da Hausawa ke yi lokacin damuna dan taimaka ma juna

Noman Gayya dadaddar gargajiya ce ta taimaka ma juna lokacin damuna inda yawancin yan gari ke gayya su je gonar wani su mishi noma ko kama mai ga aikin noma, gargajiyace ta nuna kulawa da yanuwantaka a Kasar hausa. A Jamhoriyar Nijar da wasu wurare a Tarayyar Nijeriya cikin Afruka ta yamma, inda aka fi gudanarda wannan kyakyawar tabi’ar, manoma wanda basu iya ayukkan noman da kuma wanda basuda yara kakkarfa wanda zasu kama musu kuma sunada gonakki, sune ke kiran gayya lokacin damuna ko kuma a je musu. Noman Gayya abune na “In ka yi min in yi maka”, in mutum bai zo ma wasu gayya to shi ma ba wanda zai zo mai, ko ya fuskanci karamcin mutane ga gonatai. Kuma, mata su ma wanda suke manoma in sun cike sharududda da aka gindaya bisa su ma suna kiran yan uwansu mata da abokaninsu ga gonakkinsu dan kama musu.

A lokacin Bikin Noman Gayya ana dafa ire-iren abunci masu kara kuzari; Hura da nona, Kumande, Nashe, Lalame, Kunun zaki, Kunun kanwa da Tuwo da miyan kuka, dafa dukar shinkafa da wake da yaji d.s.s dan kosarda abokai da aminnan arzukin da sunka zo gayya, kuma yawancin lokutta, har makada ake kirayowa su zo suna ma gayyar kidi dan kara musu kuzari sanda suke biyar kidin da ake da kuma yi wata irin rawa kala guda sanda suke noman.

Abdul Mailahiya Hausa

I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder and Operator at Bago Technologies. My hobbies are Reading, Travelling and Discovering.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post