Dalilai ƙaƙƙarfa da za su sa Shugaba Muhammadu Buhari ya yi Murabus

Zanga-zangar neman Shugaba Muhammadu Buhari yayi murabus sai kara kamari take inda kungiyoyi da dama suke ta kutsawa a zanga-zangar mai taken (ya komo bisa aiki) ko yayi murabus. Shugaban zai yi murabus in bai warke ba nan-da-nan, kamar yadda wasu majinginan labarai suka ruwaito.

Ya bar kasar dan kula da lafiyarshi tun tsawon kwanukka 80, kwanakki fiye da yadda shugabannin da sunka gabacesu suka taba shafewa a waje.

Ciwo nashi ya zamo wani abun bincike inda su ma na damanai cikin duhu suke.

Mataimakishi, Yemi Osinbajo, tun lokacin yake tafiyarda ayukkan kasar tun barinshi.

Wata madogara daga fadar Shugaban kasa haka kuma, ta bayyana cewa Shugaba Muhammad Buhari zai yi murabus in bai samu waraka ba nan gaba.

Majinginar tacce, “Shugaban bai iya lakema shugabanci in rashin lafiyar ta gagareshi. Zan iya gaya muku cewa ya bada adadin kwanakki in bai warkeba a lokacin, zai sa hannu a takardar murabus kuma in kun san Shugaba Buhari kwaran da gaske, mutumne wanda bai magana biyu.

“Wannan ne dalilin da yassa Yan Nijeriya wanda ke kaunar shugaban da kokari nai na maidoda martabar Nijeriya zasu cigabs da mai addu’a waraka nan-da-nan. Ba amfanine garemu in ya mutu kamar yadda wasu ke mai fata”, yacce.

Wata majingina tacce kafin Shugaban yayi tafiyar tashi zuwa United Kingdom, ya so ya bar takardar murabus ga Majalissar tarayya amman wani tsohon soja mai mukamin “General” daga Jahar Taraba ya shawarceshi kar yayi haka.

Shin Shugaba Buhari zai kafa tarihi na zama shugaban farko da yayi murabus bisa ganin dama?

Abdul Mailahiya Hausa

I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder and Operator at Bago Technologies. My hobbies are Reading, Travelling and Discovering.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post