Gatanar wani Maraye da Mugunyar Kishiyar Uwa

Wannan gatanar marayu ce.

Gatanan, gatananku. Ta je. Ta dawo.

Wani mutum ne ya mutu ya bar ɗiya maza su biyu, da uwayensu, mata biyu. Sannan cikin uwayen sai guda ta kamu da rashin lafiya. Tana shan magani, amman ciwon ya ɗi ci ya ƙo canyewa. Sanda ta ga ba makawa dai sai ta mutu; sai ta kira ƴar uwarta, waccan kishiyar tata (matar mijinta) maccen ta biyu, “Kin ga ciwon ga nawa ba zai warku ba. Nasan zan mutu, sanda Allah, maɗaukakin sarki, ya ɗauke min rayuwata daga reni, ga Ɗa nan na bar miki ƙarƙashinki, dan Allah dan Annabi.” Tacce, “Ba komi, Na ji.”

Aka zo lokacinda ranar ta zo ta mutu, shi kuma yaron bai kai girman sanin ciwon kanshi ba. Sannan aka gama bizne aka yi zaman makoki aka ƙare. Aka ja ƴan lokutta bayan rasuwarta. Yanzu ɗan ta da ɗan kishiyarta nada kaji wanda suke kiwo, yanada guda, shi kuma marayan guda.

Wata rana kishiyar ta ɗauki kare ta rabke kazar marayan lokacin da bai nan, ta bigeta da gan gan ta kasheta. Lokacinda ya dawo ya ga kaza tai matatta; bai ce komi ba sai “Kaico! Allah, maɗaukakin sarki, yau kazata ta mutu.” Ya ɗauke ta, ya figeta, sannan ya raɗaɗata, Ya aza tukunya bisa wuta, ya dafeta duka. Ya ɗauki naman ya nufi kasuwa dashi.

Duk wanda ya zo ya ce ya saida mai, sai ya ce bai saidawa, sai an bashi doki. Sannan sai ga Ɗan Sarki ya zo, ɗan lelen sarki; shi ma ɗan ƙaramin yarone. Yana bisa ƙaƙƙarfan doki; sai yacce naman wannan kazar yake so kuma doli a saida mai shi. Sai marayan yacce, in bai bashi doki ba, in dan ta shi, ba wanda zai ci naman kazar tai. Sai aka bashi dokin, shi kuma Ɗan sarkin naman, sannan sai wancan ya ja doki nai har gidansu.

Amman mugunyar kishiyar uwar da ganin dokin yazo dashi gida sai tacce, “Ja dokinka ka sa shi wancan ɗakin, ka lashe gambun da laka; cikin kwanakki bakwai, in ka buɗeshi, zaka ga yayi girman da zai fashe ɗakin.” Nufinta in yayi haka dokin ya mutu. Yanzu shi ɗan tsammanin yake da gaske take, sai yasa dokin ɗakin, ya lashe gambun. Lokacinda kwanakki bakwai suka wuce, ya buɗe ƙofa, ya ga dokin nashi ya ƙara girman gaske.

Amman sai kishiyar uwar ta ɓata rai saboda dokin bai mutu ba. Kunga, haka akai ta tafiya, sai wata ran tacce, “Yau babu damman hatsi da za’a abunci dasu.” Doli sai ya saida doki ya sayo hatsi. Amman shi sai yacce, “Yaaa ke uwata, ya ya zama doli sai an saida doki a sawo damma?” Sai tacce, “Dan ni ba uwarka bace, saboda haka kake jayayya dani?” Sai yacce, “Bani jayayya, Zan je in nemo damma.” Sai tacce, “Bari! In baka saida dokin ba ka bar kaza cikin gashinta.” Sai shi kuma marayen yacce, “Haka ba zata yuwu ba.”

Ya je ya saido dokin ya kawo damman hatsi, ya kawo mata. Ta ƙone damman duka; bata bar komi ba, sai wasu ƴan ƙanana zangarnu sunka rage. Ya ɗauke su, ya ɗimka ƴar jikka ya sasu ciki.

Da rana ta gewayo sai ya tafi wani ƙauye yawo, ya hau wani dutse wanda ba’a hawa. Sunka ganshi, suka kame shi suka ce zasu yanke maƙogwaronshi. Sai shi yacce, “Na ji labarin sarkin ku ya makance, dan saboda haka nazo ne na mai magani. In baku so sai ku kashe ni.” Amman sai sunka ce, “Muna fatan haka.”

Sai aka kawo shi gidan sarki aka bashi masabki a wani kutuɓu. Da dare yayi sai ya ɗaga zangarnan hatsin; waɗannan da wuta ta rage. Ya kunna ma zangarniya guda wuta ya gewaya bayan gidan sarki har ta mutu. Sai sarki ya fara gani dushi-dushi. Sai ya kunna wata, da ta ƙone, sai idanuwan sarkin biyu sunka buɗe. Daga nan sai aka karramashi.

Da safiya ta yi sai sarkin ya tara mutane yacce, “Kun ga yaron nan ya min magani. Makanta ta ta warke, zan bashi rabin gari ya mulka.” Sai yaron ya bada amsa, Ni dan kasuwa ne, mai wucewa, kuma bani mulki.” Sai sunka ce, In baka mulki, ka ɗauki duk abunda kake so ka tafi.”

Sai ya tattari bayi, shanu,da kyawawan abubuwa, ya tafi dasu, ya shiga garinsu dasu. Mutanen sun yi mamaki. Amman kishiyar uwar sai tacce, “Zo, mu je hanyar nan ta tabki, Na ga kusu ya shiga wani rame; ka tono min shi nai miya.” Sai shi yacce, “Yaaa ke, uwata, mi aka yi aka yi naman kusu? Ga na zabbi, kaji, da na raguna.”

Sai ita tacce, “Mun san kanada arzuki; amman ni dai, naman kusa shi nike so.” Sai shi yacce, “Ba matsala. Mu je, ki nuna min.” Ta san ramen macizai ne amman sai tace mai haka dan ta jawo mai matsala.

Yanzu sai babban bawanshi ya tashi ya rakke shi. Sai tacce, “Zamna, naga kai mai bayi, da kai kaɗai zamu je. In bazaka zo ba, sai ka tsaya.” Yanziɓu sai yacce ma bayi nai su zamna zaai tafi shi kadai. Sunka zamna. Sunka kama hanya, ahi da kishiyar uwar. Ta tafi ta nuna mai ramen.

Da zai fara hartar ramen, sai tacce, “ka aje kalmen ka zura hannunka ciki.” Sai ya zura hannunshi ya jawo sarƙa. Yacce, “Ga shi.” Sai tacce, “ba shi bane. kusu, nicce, ke ciki.” Sai ya ƙara zura hannunshi ya janyo ɗan-hannu na zinare. Amman ita sai ta hassala ta koma gida. Mugunyar kishiyar uwar sai ta kira ɗan ta; ya zo, sai tacce ya zura hannunshi ya kamo mata kusu. Da zura hannunshi sai maciji ya sari hannun, sai sunka yi kama-kama sunka kaishi gida. Ya mutu kafin su kai gidan. Ita ma mutuwa tayi cikin kwanakki ukku.

Marayen ya gadi dukiyar gidan. Wannan ne asalin karin maganan nan cewa, “Marayan dake sa ragga ake ƙyama, amman in na ƙarfe ne sai a rinƙa girmama shi.”

Shikenan.

Ƙunƙur kan kusu.

Abdul Mailahiya Hausa

I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder and Operator at Bago Technologies. My hobbies are Reading, Travelling and Discovering.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post