Hira tareda Nura M Inuwa, Tarihin shi da yanda Mahassada sun ka watsa mishi Ruwan Guba

Nura M Inuwa, ɗaya daga taurarun mawaƙan masana’antar waƙoƙin hausa, Kannywood. “Mai makogwaron zinare!” shine laƙabin da ake mai kasancewar yanada wannan muryar ɗin. A hirarsu da aminiya a 2012, tauraron mawaƙin yayi bayanai dalla-dalla gameda rayuwatai da ta sana’atai da kuma yadda mahassada sunka watsa mai ruwan guba kamar haka.

Mu fara da jin takaitaccen tarihinka.

Assalamu alaikum, cikakken sunana shi ne, Nura Musa Inuwa, amma a yanzu an fi sani na da Nura M. Inuwa. An haife ni a Kano, a 1989, kuma na yi makarantar firamare a Masaka Special Primary School, daga nan na yi makarantar sakandare a Gwammaja II. Daga nan ne kuma ban ci gaba da karatu ba saboda wadansu dalilai da suka sha karfina, wanda daga nan na fara harkar waka.

Me ya ja hankalinka ka fara waka?

Tun ina karami nake waka, wanda a lokacin ban san me nake yi ba. Wani lokaci ko da wani abu aka yi mini a gida walau na farin ciki ko bakin ciki sai na yi waka a kai. A takaice na fara waka tun ina yaro. A zahirin gaskiya ba ni da tunani na wani dalili da ya sa na fara, sai daga baya na gane cewa zan iya aika sako ta hanyar waka.

A kasar Hausa ana daukar mawaka marasa abin yi, inda har ake musu ganin masu bata tarbiyya maimakon gyara ta ko me za ka ce a kan haka?

Hmmm, duk wanda yake waka ba za a ce masa marar aikin yi ba, wani yana da abn yin amma kawai ya fi son ya yi wakar ne, sannan maganar bata tarbiyya kuma ya danganta da irin abin da shi mai wakar ya fito da shi, jama’ a suka ji. Don haka shi mawaki yana da kyau dai ya dinga fadar abin da zai amfani jama’a ba kawai abin da ya ga dama ba, sannan idan mutum daya ya yi abu a waka wanda ana ganin ba mai kyau ba ne, to su kuma masu saurare kada su dauka duka mawaka ne. A’a, shi wanda ya yi wannan abin shi ne, saboda abin da wani yake yi, ba shi wani zai yi ba.

Ana yi maka lakabi da ‘Mai Makogwaron Zinari’ ko ta ina ka samo lakabin?

Ni kaina na yi mamakin da na ji ana kira na da haka. A zahirin gaskiya masoyana ne suka sa mini sunan.

Shekara nawa ka dauka a harkar waka, kuma ya zuwa yanzu ka yi wakoki kamar nawa?

Yanzu haka ina da shekara biyar a harkar waka, kuma yanzu ba zan iya cewa ga adadin wakokina ba, amma dai ina jin wakokin da na yi za su kai 100.

Ko kana da bakandamiya daga cikin wakokinka, kuma me ya sa ka zabe ta?

Gaskiya ba zan zabi bakandamiya ba yanzu, kasancewar wakokin da aka san ni da su suna da yawa, kuma sau da yawa nakan ji a wurin mutane sukan ce wannan waka tafi, amma idan suka sake jin wata sai kuma su ce tafi. Don haka wadda mutane suka fi so ni ma ita na fi so, kafin nan gaba na fitar da bakadamiyata.

Ko za ka fada wa masu karatu kadan daga cikin wakokin da ka yi, walau na fina-finai ko na tallace-tallace ko na siyasa da sauransu?

Gaskiya duk a bangaran da ka lissafa babu wanda ban yi waka ba, kamar a fim akwai irin su ‘Rai Dai’ da ‘Aisha Humaira’ da ‘Badi Ba Rai’ da ‘Soyayyar Facebook’ da ‘Sayyada’ da ‘Zurfin Ciki’ da sauransu, amma na siyasa ba za su kirgu ba.

Sau da dama ana rade-radin rubuta maka waka ake yi, shin mene ne gaskiyar maganar?

To, a gaskiya ba a rubuta mini waka. Ni nake rubuta wakata da kaina. Sau da yawa wadansu wakokin nawa ba ma rubutawa nake yi ba.

Mutane na korafin ba ka yin kundin wakokin bidiyo, kamar sauran takwarorinka mawaka me za ka ce kan hakan?

Alhamdu lillah, mutane su yi hakuri, ina kuma sanar musu yanzu haka na gama daukar sabon kundin wakokina, kuma zai fito nan ba da dadewa ba.

Ko kana da ubangida a harkar waka, wanda ya yi maka jagora a harkar?

Gaskiya ba ni da ubangida a harkar waka, Allah shi ne Ya iya mini da iyawarSa, amma ba wanda ya koya mini waka ko kuma nake tare da shi matsayin ubangida, sai dai ina girmama Ibrahim Ibrahim domin na dauke shi matsayin yayana ba ubangida ba, kuma idan har shawara zan nema a mawaka shi ne wanda nake ganin zan iya nema a wajensa, kuma na fada matsayinsa ya wuce na ubangida yayana nake daukarsa.

Kwanakin baya an kawo maka hari har ya yi sanadiyyar kwanciyarka a asibiti. Me kake gani ya kawo hakan?

Ba ni da wani abu da nake tunanin ya ja hakan. Ni dai na dauka kaddara, kuma su wadanda suka yi su suka san dalilin da ya sa suka yi mini, amma na san ban yi wa kowa laifi ba. Na bar wa Allah komai, Shi ne zai yi mini sakayya ranar da suka manta da ita.
Ka yi wa masu karatu bayanin yadda al’amarin ya faru?
Wani ne ya kira ni ya ce zan yi masa wakar aure, wai matar da zai aura ta ce ni take so na yi mata waka, shi kuma ba mazauni ba ne, don haka ya ce in daure in zo in karbi kudi da na sunayen da za a sanya a wakar, ni kuma sai na je gudun kada ya zarge ni da girman kai, sai na je inda ya fada mini. Daga nan ban san hawa da sauka ba sai na ji saukar sinadarin acid a jikina.

Wane buri kake so ka cin mawa a harkar waka?

Nagode Allah, ko iya nan na daina waka ba ni da wani buri face abin da Allah Ya nufa, komai na zama Allah ne ya kai ni. Dan haka Shi Ya san matsayin da zai kai ni a gaba.

Wacce shawara kake da ita ga ‘yan fim da kuma sauran mawaka?

Mu cire hassada a cikin ranmu, yadda za mu samu hadin kan da na kasa zai dinga girmama babba shi kuma babba ya kare mutuncin na kasa. Wannan ita ce shawarata.

Daga karshe, mene ne sakonka ga masoyanka?

Ni dai kodayaushe ina so masoyana su sani ba ni da kamarsu, domin da su nake alfahari. Ina mai gode wa Allah da Ya ba ni su kuma ina kaunarsu kamar yadda suke so na, kai fiye da hakan ma. Don haka ina rokon afuwa ga wanda na sabawa ba tare da na sani ba. Dan Allah masoyana ku zamo masu yi mini uzuri a kodayaushe ko da an ce Nura kaza, kada ku dauka, ku gani da kanku sannan ku yarda. A karshe ina yi muku godiya da fatan Allah Ya bar mu tare.

Abdul Mailahiya Hausa

I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder and Operator at Bago Technologies. My hobbies are Reading, Travelling and Discovering.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post