Ire-iren Musulmai 5 da kallon da su ke ma Sallar Taraweeh lokacin Ramadan

Ramadan watane mai yawan albarkoki kuma watane wanda cikin shi aka sabkarda Al kur’ani Mai Girma zuwa ƙasa dan mutane daga Aljannah. A nan mai rubutun yayi magana kan sallar Taraweeh, amman abun dubi shine ire-iren surorin da Limamai ke karantawa wanda ke sa wasu gudu, maimakon surori kamar Nas, Falaq da wasu taƙaitattu, sai ku ji Liman ya jawo su Yasin, Harma da wasu masu tsawo, duk da cewa ƙa’idar sallar ce.

Ahmadox ya hauda cewa a Nairaland, “Kawai dan in ƙara muna sani kaɗan, Na tattaro jerin mutane danganeda kallon da suke ma raka’o’i goma zuwa sha huɗu na sallar nafilar Taraweeh lokacin watan azumi Ramadan.”

 1. Musulmai lokacin Ramadan kaɗai:
  Waɗannan jerin mutane sune dalilin cikar Masallatai lokacin Ramadan. Mai yuwuwa basu halartar sallah kafin Ramadan. Suna cewa wai sallah wuya gareta, amman sai ƙaunar Salla da Taraweeh ta shiga zuciyarsu lokacin Ramadana.

 2. Musulmai masu dabo:
  Wannan jerin mutanen kullum kamar wutar NEPA suke. In kun gansu yau, to karku yi tsammaninsu gobe.

 3. Masu jinƙirin zuwa Taraweeh:
  Wannan mutanen basu halartar Isha, suna isowa Masallaci sanda Taraweeh ta kusa ƙarshe. Su yi sallarsu ta Isha sannan sai su bi sahun Taraweeh na kusan ƙarshe kuma shikenan!

 4. Masu tafiya tun da wuri:
  Waɗannan akasin masu jinƙirtowane. Suna isowa da wuri a yi Isha da su sannan sai su wucewarsu nan da nan bayanta, babu ruwansu da Taraweeh. Na jin kumyar cewa ina fadawa wannan jerin wani bi, saboda surori masu tsawo.

 5. Ƴan ba ruwansu:
  Su basu ma zuwa Masallaci kwata-kwata dan ko sallatar Taraweeh ko Isha ɗin

Duk jerin da kunka tsinci kanku, in ma akwai, ku dai ku san sarai cewa nauyine gareku na cike sharɗoɗin addini kullum-kullum, ba wai sai ga watan Ramadan ba kaɗai. Yadda muke azumtar wannan wata mai Albarka to muna fatan Ubangiji Allah ya amshi ibadun mu. Ramadan kareem

Abdul Mailahiya Hausa

I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder and Operator at Bago Technologies. My hobbies are Reading, Travelling and Discovering.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post