Labarin Baƙon da ya juye Taimakawa gurɓata Tarbiyyar cikin Gida

An kwaɗaita muna girmama baƙi a rayuwarmu ta kullum, kamar yadda addinan mu sunka koyarda da kuma mutumtaka irin ta mutane, amman kishiyar haka takan abku, wato basu baya dan zasu iya juyowa ta kowane lokaci su zama masu taimakawa wajen gurɓata tarbiyar cikin gida. Wannan labarine kan wani baƙo da yai kaka gida cikin gidajen mu, yanada ban ƙayatarwa, karantarwa da kuma shaƙatarwa. An ɗaukoshi daga islamcan.com.

“Ƴan watanni kafin a haifan, babana ya gamu da baƙo wanda sabon zuwane gidan mu a Abagana kasancewatai muslimi baban nau. Da farko dai, Baba ya ƙayatu da wannan baƙon, sannan ya gayyatoshi dan ya zamna cikin gidan mu. Baƙon ya samu karɓuwa da gaggawa sannan kuma yana daga wanda ke shirin mini maraba a doron ƙasa bayan ƴan watanni. Tun sanda na tashi ban taɓa tambayar zamanai cikin gidan mu ba. A tunanina na yaranta, kowane ɗan gida nada nashi ɓangaren aiki na daban. Magajina na wajen uwa, Lawali, shekaru uku an garai gabana, tunanin mu guda. Halima, kaunata, itace nike wasan “ƙauna da wa” da ita kuma nike nuna girmantaka. Uwayena mutanene masu umurta matuƙa- Inna ta koya min son Allah, kuma

Babana ya koya min yadda zan girmamashi da shi da manzonai (S.A.W). Amman baƙon ɗan gatanan mune. Zai iya ƙirƙiro labarai masu ƙayatarwa. Jarumtaka, tatsunniya da barkwanci sune kan gaba. Zai iya riƙe ƴan gidanmu duka ya kaisu dogon zango na ƴan sa’o’i ko wane maraice. In ina son ƙarin haske game da sanin siyasa,

tarihi, ko kimiya, ya san dasu.

Yanada sanin abubuwanda sunka gabata da kuma gane na yanzu. Kamannin da yake zanowa nada kaman gaskiya da nikan yi dariya ko kuka sanda nike saurare. Kamar aboki yake ga ƴan gidan. Yana garzaya Baba, Lawali da ni zuwa wasan da muka fi sha’awa. Yana kwaɗaita muna kallo kullum da kuma yin mai yuwuwa na haɗamu da sanannun mutane.

Baƙon wani irin masurucine. Baba bai damuwa amman wasu lokuttan Inna takan tashi- sanda mu kuma ya kame mu da wasu daga labarai nai na dogon zango ta shiga ɗakinta, tana karanta Alqur’ani Mai Girma.

Na yi tunani ko ta taɓa roƙon baƙon ya wuce. Kun gani, babana na kyautata tarbiyan gidanai ta bamu tabbatattan koyarwa ta musamman. Amman wannan baƙon bai ganin cewan ya kiyaye su. Ɓatanci, misali bai samu gindin zama gidanmu ba ko da daga garemu ne, daga abokai, ko manya. Daɗaɗɗen baƙonmu, duk da haka, yana taka wannan dokar da ƴan maganganu ƙalilan ya kuma sa baba ya kaɗu. Iyakacin sanina dai baƙon ba’a taɓa shi. Babana mai gudun giyane wanda bai yarda da giya gidanai – ko da ga girkine.

Amman baƙon yana ganin cewan muna buƙatar sani sai ya ƙara sanar damu zuwa wasu ɓangarori na rayuwa. Yana kwaɗaitamuna giya da wasu kayan barasa so so.

Yana daɗaɗa muna taba, taba ta mazace, shisha kuma ta musamman. Yana surutainai ba ƙaƙƙautawa

(da yawa ba ƙaƙƙautawa) game da saduwa. Sharhukka nai wasu lokutta na gaskiya, wani bi kuma marar dogaro kuma na ɓacin rai.

Na sani yanzu cewan farkon sanina na zamantakewar namiji da macce aikin wannan baƙon ne.

Da na waiwaya baya, na gano cewa dai ikon Allah ne yassa bakon bai rinjayemu ba ƙwarai. Lokaci bayan lokaci ya hi karhin uwayena. Duk da haka ba’a taɓa daga mai ƙafa ba ko kuma kora tai. Hiye da shekaru ishirin da biyu da sunka wuce tun sanda baƙon ya zowa ƙaramin gidan.

Ba a cika kulashi ba kamar yadda ake yi yan shekarun baya. Amman in zan shiga ɗakin uwayena yau, zaku ganshi zamne bisa ɓangerenai, cikin jiran mutane su saurareshi sanda yake ratato surutai ya kuma kai mutum dogon zango.

Sunanshi kuke tambaya?

Muna kiranshi akwatin TV

Ya saku dogon tunani, ko ba haka ba?

Abdul Mailahiya Hausa

I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder and Operator at Bago Technologies. My hobbies are Reading, Travelling and Discovering.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post