Ohaneze Ndi Igbo ta yi ma Taskar Matasan Arewa (AYF) gargaɗi

  Mataimakin mai magana da yawun bakin Ohanaeze Ndigbo, Mr. Chuks Ibegbu, yayi kira ga “Department of State Services” (DSS) da na jami’an ƴan sanda, cewa su ɗauki ƙwaƙwaran matakin kare niyyar kaima Inyamurai dake zamne a Arewacin Nijeriya hari.

  Ibegbu yana maida martani ga yunƙurin da Ƙungiyar Matasan Arewa ta yi mai taken “The kaduna declaration” ga duk ƴan ƙabilan Igbo dake zama a Arewacin ƙasar cewa su yi ƙaura zuwa garuruwansu na asuli cikin ƴan watanni ukku.

  Ibegbu, wanda ke kallon jawabin a matsayin ƙin jini, ya nemi jami’an tsaro na su kama jikinsu kafin a kawarda Inyamuran dake zamne a Arewa.

  Yacce, “DSS, Ƴan sanda da sauran jami’an tsaro na su kallato jawabin ƙin Inyamurai da Taskar Matasan Arewa da na wasu Ƙungiyoyin na Arewa ke aikowa.

  “Ba za’a yi watsi da maganar ba; ƙwaƙwaran mataki za’a ɗauka na durƙushe ƙudirin hari ga Inyamuran dake Arewar. Haka ta faru a baya kuma ba zamu so ta ƙara faruwa ba.

  “Gaskiya, Dole DSS su yi gaggawar kame Yerima Shettima. Mun zura ido dan ganin yadda DSS zata yi ga wannan lamari.

  “Yawabin Shettima na ƙin jini ne; ya nuna bambamcim ƙabila kuma mun sani cewa irin wannan kalamai na iya jawo yaƙin basasa. Jawabanshi na iya wargaje ƙasar ga.”

  Madogara: Dailytrust

Abdul Mailahiya Hausa

I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder and Operator at Bago Technologies. My hobbies are Reading, Travelling and Discovering.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post