Sabkar Shugaba Muhammadu Buhari cikin Kamannai (Photos)

Shugaba Muhammadu Buhari da ƙarshe Allah yasa ya sabka Abuja lami lafiya bayan ya kwashe kwanukka fiyeda 100 a Birnin Landan, United Kingdom, inda yaje neman magani tun ran 7 ga watan Mayu.

Jirgin fadar shugaban ƙasa da ya kawo Shugaban ya sabka a ɓangaren shugabanni a filin sabkar jirgin sama na Abuja, Nnamdi Azikiwe International Airport, Abuja, wajen karfe 4.35 na rana.

Shugaban ya sabko daga jirgin samar, ƙirar NAF 001, wajen ƙarfe 4.48 na rana.

Ya samu tarbe daga manyan jigajigan gwamnati ƙarƙashim Mataimakin shugaban ƙasa, Yemi Osinbajo.

Shugaban ya sanyo kaftan ruwan ƙasa-ƙasa, ya hau rostrum ya karɓi gaisuwar ban girma ta ƙasa daga Brigades of Guard.

Bai kulada ɗimbin masu gadi da aka jera mai ba na girmamawa kafin ya shiga gidan shugabanni tareda tawagar sunka tarbeshi.

Filin sabkar jiragen tayi tsit sanda ma’aikata suka yi ƙoƙarin samun ganinshi.

Source punchng.com

Abdul Mailahiya Hausa

I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder and Operator at Bago Technologies. My hobbies are Reading, Travelling and Discovering.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post