Saƙon Shugaba Muhammadu Buhari zuwa ga Ƴan Nijeriya - A'isha Buhari

Matar Shigaban ƙasar Nijeriya, Mrs Aisha Buhari ta sabka a filin sabkar jirage Nnamdi Azikiwe International Airport, Abuja ran Talata 06/06/2017 tareda mataimakanta da danginta daga United Kingdom inda taje ganin mijin nata, wanda yayi balaguron kula da lafiyarshi a birnin Birtaniya. Ta isarda saƙon Shugaba Muhammadu Buhari ga Ƴan Nijeriya dangane da addu’o’in da suke mai da kuma cewar nan bada daɗewa ba zai dawo ƙasar.

Mai magana da yawun Malama Buhari, Suleiman Haruna, cikin bayani nai yacce Matar Shugaban ƙasar, da sabka, ta isarda godiyar Shugaba Buhari ga Ƴan Nijeriya.

Matar Shugaban ƙasar ta faɗama Ƴan Nijeriya cewa Shugaba Buhari yana samun sauƙi ƙwarai kuma tacce shugaban na miƙo godiya tai ga Ƴan Nijeriya yawanci ga Shugaba da aka barma gado, Professor Yemi Osinbajo dan tsayin daka da yayi ga ƙudurorin ƙungiyarsu All Progressives Congress, APC, da kuma addu’o’insu dan warkewatai nan da nan.

Malama Buhari ta ƙara da cewa Shugaban ya nemi haɗin kan Ƴan Nijeriya da Shugaban dake bisa gado, Osinbajo, na tabbatarda alƙawurran da APC ta yi lokacin yaƙin neman zaɓe kamar yadda yake rubuce ga kundin ƙungiyar dan alƙawurran Sauyi ga Ƴan Nijeriya ya tabbata.
“Na godema Allah ga sabkar tafiyata U.K, inda na ziyarto Shugaba Buhari.” Ya godema Ƴan Nijeriya dangane da addu’o’insu ga lafiyarshi da kuma jajircewarsu na jure cecekuce.

“Shugaban ya godema Shugaban dake bisa gado, Prof. Yemi Osinbajo ga biyayyatai da kuma kiran Ƴan Nijeriya na su cigaba da marama mai baya ga ƙoƙari nai na tabbatarda umarnin ƙungiyarsu All Progressives Congress.”

“Yana neman haɗin kanku matuƙa da biyayya ga Shugaban dake bisa gado dan a cimma ƙudurorin wannan mulkin kamar yadda yake rubuce ga kundin mu na APC, dan mu gina ƙaƙƙarfar cigaba ga kasar mu Nijeriya,” Tacce.

Mrs. Buhari ta yi balaguro a 30 Mayu zuwa UK dan yin ƴan kwanakki da Shugaban.

Buhari ya bar Nijeriya a 7 ga Mayu dan kula da lafiyarshi a karo na biyu cikin ƴan watanni.

Madogara: Vanguard

Abdul Mailahiya Hausa

I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder and Operator at Bago Technologies. My hobbies are Reading, Travelling and Discovering.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post