Takaitaccen tarihin Faruk M Inuwa da wakar shi ta farko

Faruk M Inuwa ƙaramin yaron mawaƙin hausa ne da yayi ma kainai suna a masana’antar waƙoƙin Kannywood. Ɗan makarantar ya gwammacema yin waƙoƙinai shi kaɗai- ba tareda ya haɗa da muryar mata ba ga yawancin waƙoƙinai, kamar yadda takwarorinai ke yi kuma yawancin waƙoƙinai kan soyayyane da aure. Kundin waƙoƙin da ya haskakashi shine “Soyayyace” wanda ya haɗa ƙarƙashin ƙasurgumin mawaƙin hausan nan da ya ciri tuta, Nura M Inuwa, mai gidanshi kuma jagaba ba magajinaine ba kuma basu haɗa Uba ɗaya dashi ba balle su zama ƴan gida guda, kamar yadda masoya ke ƙwanƙwanto, kasancewar sunada sunaye kusan guda.

Faruk M Inuwa haifaffen Gadon kaya ne, wani gari ƙarƙashin ƙaramar hukumar Gwale ta jahar Kanon tarayyar Nijeriya. Yanada shekaru 23 da haihuwa. Yayi karatun Addini da na Boko duk a garinsu kuma har yanzu yana karatu a Jami’ar Aminu kano collage of education.

Faruk M Inuwa yacce ya fara da koyon kiɗi kafin shiga harkar waƙoƙi, bayan abokai na ganin kamar ba zai iya ba, inda yanzu haka waƙoƙin sun kai kusaa 300 a hirarsu da sarauniya.

Waƙatai tq farko itace wata waƙa da ya yima Margyayin Sarkin Kano, Sarki Ado Bayero. Allah ya jiƙanshi da rahama. Ameen.

Faruk M Inuwa ya zayyano ”soyayyace” a matsayin bakandamiya cikin waƙoƙinshi su 300.

Abdul Mailahiya Hausa

I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder and Operator at Bago Technologies. My hobbies are Reading, Travelling and Discovering.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post