Takaitaccen Tarihin Fati Washa da Kyawawan Kamannan ta (Photos)

Fati Washa mai son sana’ar shirin kwaikwayo ce tun tana ƙarama. Kasancewarta mai taimakama jarumai bai durkushe tauraruwarta ba. Kyakkyawa kuma doguwar jarumar, wadda ta banƙara tsakanin manya ake damawa da ita tun farkon shigowarta masana’antar kannywood. Matsayin da ta hau a cikin shirin Hindu – An African Extra Vagrant haƙiƙa abun yabawa ne, ta bakin Hausafilm.

Shirin da ta fito a tsakkiyar manyan jarumai irinsu Adam A. Zango da Jamila Umar Nagudu. Yanayin yadda ta taka rawa a tsakkiyarsu tamkar ba macce ba ya ƙayatar da makallata. A wasu lokutan ma sai mutum ya mance da cewa macce yake kallo, dan ta yi tsayiwar daka wajen tabbatar da ganin ta taka muhimmiyar rawa a matsayinta na Bokanya.

Haka zalika batun kasuwa nan ma babu magana, dan tun bayan nuna shirin a Gidan kallon dake bisa hanyar Zoo Road a Kano, makallata sunka nuna maitarsu a fili ta mararin kallon shirin. Har ila yau ta samu yabo daga wajen manyan masana shirin kwaikwayo irin su Prof Abdallah Uba Adamu, Ahmad Gidan Dabino.

Fati Washa a jajircewarta a kannywood ta samu karramawa da shaidar yabo da dama a matsayinta na jaruma mai kwazo a shirin kwaikwayon da ta taka rawa. Kuma ƙarawa da ƙarau, Allah cikin rahamarshi a shekarar 2016 ya bata ikon zuwa Umrah a Saudi Arabiya.

Abdul Mailahiya Hausa

I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder and Operator at Bago Technologies. My hobbies are Reading, Travelling and Discovering.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post