Takaitaccen Tarihin Mai zazzaƙar murya, Umar M Sharif da Masoyiyar shi ta farko

Umar Muhammadu Sharif na ɗaya daga mawakan Hausa masu zazzaƙar murya wadanda Ubangiji Allah ya yi ma baiwar waƙa, tarmamuwar shi na haskawa a harkar kuma ya samu kyaututtuka da dama kan harkar. Abokin Nura M Inuwa ne na kut da kut. Ɗan garin Rigasa dake Kaduna ne, haifaffen shekarar alib dari tara da tamanin da bakwai 1987 ne (shekara 33). Ya yi karatun matakin farko da na gaba, wato sakandare duk a garin na su, Rigasa.

Umar yacce ya kasance ɗan makaranta mai ƙwazo lokacin karatun shi na sakandare kuma yacce shi ya ɗau tafarkin shi (Islam) da hannu biyu-biyu. Abunda ya tsunduma shi a harkar waƙa shi ne wani abunda ya faru tsakanin shi da masoyiyar shi wadda ya fara soyayya da ita, kamar yanda ya bayyana ma Gidan Radiyon BBCHausa yayin hirar su.

Umar M Sharif ya sha shadda

Wata rana sanda i na ɗan sarmayi, dakwai wata yarinya wadda ni ke matuƙar so da ƙamna a unguwar mu, amman kasancewata sabon shiga sai ni ke jin kumyar tunkarar ta dan mu yi zance.

Umar M Sharif tareda abokiyar aikin shi Fati Niger

Ya ci gaba, bayan na shaida ma abokai na, sai sun ka shawarce ni da in yi tattaki har gidan su, wato in je gidan su in aika ta zo. Na yi haka, amman duk lokacinda ta fito dan fuskantan mai kiran ta, ba wanda ta ke tarardawa a kofar gidan na su ballantana wanda an ka ce ya na kiran ta. Ni kuma a lokacin i na wani ɓangare i na wasan ɓoyo na soyayya. Na yi haka kusan so ukku. Sannan, ana nan sai wata rana nicce yau zan yi tsayin daka dan in ga abunda zai ture ma buzu naɗi. Sanda na isa ƙofar gidan su kamar kullum, na aika ma ta ta zo i na kiran ta, amman yarinyar ta ki ta fito, wata matsala sabuwa kuma. Sai na tuno yanda na yi wasa da hankalin ta na gano ba za ta zo ba dai. Yayinda ni ke nan i na cikin jiran kiran da ba amsawa, sai hawaye sun ka kwararo jikin kumatu na, a wannan halin na tsinci kai na i na rera waka (ita ce waka ta ta farko). Daga nan na yi ta waka har kofar gidan mu. Umar ya ce ya kan rera waƙa duk lokacinda ya tuno abun. Sannan kuma dama dakwai abokin wan shi wanda shima mawaƙi ne, ya saurari wakar shi wata rana, ya ya ba shi shawarori game da waƙa ya kuma taimaka mishi wajen haɗa wakar shi ta farko a dakin kidi.

Umar M Sharif yacce ya na da fiye da wakoki 500 inda ya zanyano; Duniya Ce, Nadiya, Madubi, Jinin jikina, Mai atamfa, Bakandamiya da Babbar yarinya a matsayin bakandamiya. Umar M Sharif bayan ya kasance shahararren mawaki, dan wasa ne kuma mai shirin wasan kwaikwayo ne a masana’antar Kannywood. Shirin da ya fito ko ya shirya sun haɗa da; Mahaifiyata, Nas, Jinin jikina, Ba zan barki ba, ka so a soka d.s.s

Yaran Umar M Sharif

Yayin da an ka tambaye shi zancen iyalin gida, ya ce ya na da aure da ɗiya kusan biyar. Kwanan baya mun ga a kafar Instagram, inda ya hauda cewar ya na samun sauki bayan hatsarin da ya samu. DanZubair ɗaya daga dubban masoyan ka na ma ka fatan sauƙi cikin gaggawa daga GobirMob.com.

Abdul Mailahiya Hausa

I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder and Operator at Bago Technologies. My hobbies are Reading, Travelling and Discovering.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post