Tarihin Mawakiyar Kannywood, Fati Niger da adadin dukiyarda ta mallaka a Masana'antar

Fati Niger, sanannar mawaƙiyar hausa ce da Allah yayi ma zazzaƙar muryar da bata ɓoyuwa. Ta samu sarautar “Gimbiyar mawakan hausa” a ƙarshen shekarar 2016 a Borgu, Jahar Niger. Tun kafin wannan, masoyanta kema mawaƙiyar kannywood ɗin, yar shiri, mai bada umarni da mai shirin wannan sunan. “Girma-Girma” itace waƙar da tafi ɗaukakata, kuma waƙarta ta farko tun lokacin. Amman abun takaici ta yi koken cewa waƙar bata kawo mata fiyeda N10,000 ba saboda muguntar masu satar fasaha.

Fati haifaffar garin Wurno ce, amman ta girma a shiyar Zarya a Jahar Maradi, Jamhoriyar Niger, inda kuma ta yi karatunta na Al kur’ani. An fi saninta da Fati Niger kasancewarta haifaffar Nijar da “Fati” daga (Fati Muhammed), wata jaruma da ta taɓa haskakawa a baya, duk da cewa tabbataccen sunanta shine Binta Labaran. Kyakyawar maccen ta samu kanta a kannywood bayan ziyartar magajiyarta a kano a shekarar 2004 inda tun lokacin take jan zare a masana’antar.

Mai zazzaƙar muryar da bata ɓoyuwar ta zarce shekara 10 a kannywood. Waƙoƙinta sun wuce 500. Ta tsunduma a shirin kwaikwayo kuma shirin da ta bugo sune “kudiri” da wasu 2, ta kuma taka rawa ga wani shiri mai suna “Sakatare” a maysayin babbar jaruma. Tana harkar rerama Ƴan siyasa a Nijeriya waƙoƙi k.m.r Tsohon Gwamnan Jahar Jigawa, Alhaji Sule Lamido d.s.s.

Fati Niger ta mallaki fiyeda dukiya a kannywood dan duk inda ta sa ƙafarta ta je, masoyanta zasu rinƙa kallonta da idon ƙauna gami da arzukin duniyar da ta mallaka, sai dai batada aure- har yanzu bai zo ba. Tanada ma’aikata Girma-girma kreative limited, maka-makan gidaje a kano da sauransu, motoci kyawawa da gungun ma’aikata ƙarƙashin harakar bunƙasassar kasuwancinta. Binta ta sami rabon yin Hajj da Umrah, ɗaya daga shikashikan musulumci. Itace ginshiƙin danginta ganin ta taimaka musu kuma tana cigaba da taimakawa.

Abdul Mailahiya Hausa

I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder and Operator at Bago Technologies. My hobbies are Reading, Travelling and Discovering.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post