Ƙungiyar Fulani Miyetti Allah za ta maka Gwamnatin Taraba Kotun koli ta Duniya

A shekarar da ta gabata Chief Femi Falana (SAN), wani sanannen mai Gwagwarmayar kare Yancin Dan Adam ya kai kara a Kotun duniya mai adalci “International Court of Justice” (ICJ) a Hague da kuma Kotun ECOWAS, dangane da kishan kyashin da Fulani makiyaya ke ma manoma da wanda basu ji basu gani ba a Yankin Jukun, wanda ke Gusumci da Tsakkiyar Jahar Taraba.

Sai muka ji cewar a sati mai zuwa, kungiyar Fulani makiyaya, Miyetti Allah da ke Nijeriya zata shirya shigar da kara a gaban Kotun hukumta manyan laifukka ta duniya wato “International criminal court” (ICC) dake a Hague, a Kasar Netherland bayan wani sabon rikici da ya sake barkewa baya-bayan nan, tsakanin Fulani makiyaya da Mambilawa manoma a Mambila.

Kamar yadda labari yake a shafin BBC Hausa, kungiyar Fulani ta kasa wato Miyetti Allah ta yi zargin cewa an yi ma Fulanin kisan kyashi a Mambila dake karamar hukumar Sardauna a Jahar Taraba. A satukkan da sunka gabata ne dai aka yi ta samun rikici wanda ya danganci na kabilanci tsakankanin Fulani da Mambilawa.

Inda alkalamu marar tabbas sunka ce mutane kimanin dubu daya sun mutu sannan an kashe dabbobi fiye da dubu ukku. Kungiyar GanAllah ta ce tana zargin Gwamnatin Jahar da hannu a rikicin.

To sai dai Kwamishinan yada labaria na Jahar ta Taraba, Anthony Danburam ya musanta dukkan zarge-zargen, yana cewa babu hannun Gwamnatin Jahar Taraba a ciki.

Lauyan da zai jagoranci gabatar da karar a kotun ta duniya, Professor Yusuf Dankofa ya shaidama BBC cewa suna da shaidar cewa Gwamnan Jahar da kakakin majalisar sun yi kalaman da suka tunzura mutane.

Hassan Ahmed ya kuma kara da cewa ba su gamsu da matakan da Gwamnatin Jahar Taraba ke dauka ba dan dakule rikicin.
Sannan kuma kwamitin da jihar ta kafa ba ta tunanin za ta yi ma yan Fulani adalci saboda babu wakilcin Fulanin a kwamitin.

Rikici tsakanin makiyaya da manoma dai a Jahar Taraba ya dade yana wanzuwa. Sai dai kungiyar GanAllah ta Fulani ta ce kisa ne irin na kiyashi ake shiryawa dan kawar da Fulani da dabbobinsu a Jahar.

Abdul Mailahiya Hausa

I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder and Operator at Bago Technologies. My hobbies are Reading, Travelling and Discovering.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post