Za'a fara saida shinkafa a farashi mai rahusa a Birnin Ikko saboda Bikin Sallah Babba mai zuwa

Gwamnatin Jahar Lagos ta sanarda cewar zata fara saida shinkafar lake rice ran Alhamishi, 24 ga watan Agusta a wurare dabam-dabam a duk fadin jahar saboda bikin sallah babba mai zuwa ta 2017.

Kwamishanan Noma na Jahar ta Lagos, Hon Oluwatoyin Suarau, wanda ya bayyana haka a ma’aikatar shi a Alausa dake Ikeja, yacce Gwamnan Jahar Lagos, Mr Akinwumi Ambode ya jarje wasu wurare dan kaiwa da kuma saida shinkafar.

Wadannan sun hada da kananan hukumomi 57 da wuraren hukumomin habbaka noma; Agricultural Development Area Complex, Oko-oba, Agege; LTV Blue Roof Complex, Agidingbi, Ikeja, da wasu wurare na musamman a fadin jahar.

Ya kara da cewa kudin farashin zai cigaba da zamana N12,000 ga buhu mai nauyin kilo 50, N6,000 ga mai nauyin 25, da N2,500 ga mai nauyin kilo 10.

Ta bakin kwamishanan, shinkafar ta duk Yan Lagos ce mazmna da Yan-kasa, ba tareda bambamcin addini ko kabila ba.

Ya ƙara jaddada cewa shugabancinsu na yanzu zai cigaba da kiyaye aiwatuwar abubuwa da tabbatarda farashi mai rahusa.

Abdul Mailahiya Hausa

I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder and Operator at Bago Technologies. My hobbies are Reading, Travelling and Discovering.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post