Kabilun Ibo, Inyamurai zasu sha wahala in neman Biafra ya tabbata - Rev. Fr. Ejike Mbaka

Malamin Majami’ar Katolika dake zamne a Jahar Enugu, Rev. Fr. Ejike Mbaka, ya bada nashi ra’ayi danganeda neman ballewar da Yankin Nijeriya na Kudu-maso-gasas ke yi daga Kasar su zama Jamhoriyar Biafra.

Yayinda yake maganada gungun Ƴan Kabilar Ibo a East London, Babban Malamin ya ce Inyamurai sune ƙasa in sunka nemi rabuwa da Nijeriya.

Yacce:

“Babu yawancin Hausawan dakeda wata ƙaddara a Kasar Ibo. Babu yawancin Yarabawan dakeda wata kaddara a Kasar Ibo. Amman kashi 60% na harkokin kasuwanci a Arewacin Nijeriya na Ibo ne. Kashi 40% na harkokin kasuwanci a Yammacin Nijeriya na Ibo ne.”

Mbaka yayi tsokaci cewa Ibo zasu yi asara babba in kasar ta ɓalle. Ya yi iƙirari da cewa ya san abunda Inyamurai sunk mallaka a faɗin Nijeriya dan saboda ana yawan gayyatoshi ya yi addu’ar sanya albarka ga buɗa kasuwancin na Inyamurai, so da dama a Arewacin Nijeriya. Yacce:

“Ku je Sabon Gari a Jahar Kano ku ganema idanuwanku abunda Kabilar Igbo ta mallaka a can”.

Ya ƙara da cewa zasu yi koken basuda dama a gwamnati, amman karkashin Shugaban da ya gabata Goodluck Jonathan, Ibo ne ministan kudi, Gwamnan asusun kasa, da sauransu.

Ya ƙara da shawarta cewa Inyamuran da aka sanyawa zuwa neman Biafra ga Nnamdi Kanu, shugaban keɓaɓɓar kungiyar Indigenous People of Biafra (IPOB) “su diyan talakkawa ne”, wanda a nashi ganin, basuda kaifin tunanin hango abunda ake nufi da rarrabuwar kawuna. Mbaka yacce waɗannan mutanen, Kanu yaudararsu ne kawai yake.

Mbaka ya ƙara da abunda zai abku in Biafra ta zama kasa mai cin gashin kanta. Yacce:

“In kuna ganin muna fama da matsala a Nijeriya yau, zamu ga matsala a Nijeriya. Ba dan Jahar Anambra da zai so Mutumen Enugu ya zama shugaba, ba dan Imo da zai so Mutumen Abakaliki ya zama shugaban”.

Ya yanke hukumci cewa waɗannan rigingimun dake wakama a garuruwan Inyamurai dabam-dabam zasu kunno kai in Biafra ta tabbata. Sanda aka kalubalanceshi ga magana kan siyasa, Mbaka ya maida da cewa “siyasa sashine na zaman duniya” kuma “Na karanci kimiyar siyasa da Zurfin ilimin siyasa”. Ya kara da cewa ƙudurorin da aka yanke ta siyasa na shafar kowa da kowa.

Abdul Mailahiya Hausa

I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder and Operator at Bago Technologies. My hobbies are Reading, Travelling and Discovering.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post