Cikakken Bayanin Shugaba Muhammadu Buhari na cikar Nijeriya shekaru 57 da samun yancin kai

Ranar 1 ga watan Otoba ranace ta musamman ga yan Nijeriya saboda wanna na nuna ranar da munka samu abunda Diyan Adam ke makutar bege — yanci.

Tun shekarun da sunka shude kasar ta sha fadi-tashi da wasu yan matsaloli, amman 1 ga watan Otoba kullum ranar murnace.

Ranace ta godiya, dogon hange da dada sadaukantaka.

Kuma ranace ta tuni. Mu rinka tunama kanunmu tafiyarda munka yi tun 1999 – 2015, lokacinda kasarmu ta markado zuwa turbar shugabancin demokradiya.

Kuma, duk da cewa farashin mai ya kasance $100 ga kwatankwacin ganga guda da kuma ganguna 2.1m a rana, wannan ma babban arzuki ne kuma an yi watsi da wadatar zamantakewa da ayukka hannu.

An barmu da asusun kasa kwango kuma da rashin ayukka.

Kudurorin Gwamnatin APC lokacin yakin neman zabe na kira ga tabbatarda tsaro, daidaita tattali arzuki da yaki da cin hanci duk ba abun ki bane.

Doli a fara da tsare kasa. Tattali arzuki shi ma doli a daidaitashi dan karmu dogara da mai shi kadai. Doli mu yaki cin hanci da rashawa wanda shine babban makiyin Nijeriya na daya. Shugabancin mu na aiki ga shawa kan wadannan matsalolin duka.

A shekaru biyu da sunka gabata, Nijeriya ta yi gagarumin nasara a yancin siyasa. Jam’iya mai riko na rasa zaben Gwamnan Jaha, Majalissar tarayya ta kasa harma da Majalissar tarayyar Jaha ga Jam’iyyar Adawa sabon abune ga Nijeriya. Kari da cewa wannan yancine na abokantaka, riko da tabbatarda ra’ayoyin mutane. Wannan cigaban duk na nuni da cewa an samu gagarumin cigaba ga siyasar kasar. Amman kamar wadansu abubuwa na cigaba, wannan ma na tareda banna.

Dangane da kiraye-kiraye na sake ma kundin tsarin mulki gyaran fuskaRecent, abun a tsari yayi daidai, ammam yasa kungiyoyi na neman wargaza kasar. Ba zamu yarda da wadannan abubuwan ba.

A matsayina na Ƙaramin Jami’in tsaron Soja, na yi tsayin daka tun daga farko na durƙushe yaƙin basasa wanda yayi sanadiyar kashe mutane miliyan 2, da rushe-rushe da wahalhalu iri-iri. Waɗanda ke neman a sake yakin nasan ba’a haifesu a shekarar 1967 ba kuma basuda tabbacin gameda rikicin basasar da munka ci karo dashi.

Na yi matuƙar mamaki ganin cewa shugabannin waɗannan garuruwan basu jama yaransu kangararru kunnai ba ga abunda ƙasar ta sha fama dashi. Wanda basu nan su gayama wanda basu nan, illar irin wannan wautar.

*Cikin gyara*

Abdul Mailahiya Hausa

I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder and Operator at Bago Technologies. My hobbies are Reading, Travelling and Discovering.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post