Kamannai: Nadin Sarautar shahararren Dankasuwar Maradi a Tsibirin Gobir

A ranar lahadine daidai da 24 ga watan Dicemba 2017 aka yi wankan sarautar Elhj Sani Bala Dansani a Tibiri Gobir. Sani Bala shahararren dankasuwa ne kuma dansiyasa a Jahar Maradi, Jamhoriyar Nijar. Sani Bala ɗa ne ga margyayin dan kasuwa a jahar, cewa da Elhj Bala Dansani, Allah ya jikanshi da rahama.

An naɗa Sani Bala Dan garan Gobir wadda da alamu sarautace tasu ta gado. Manyan bakin da sunka hallara a taron sun haɗa da sarakan Gobir daga Nijar da Nijeriya, Jami’an Gwamnati, Yan Siyasa da Yan Kasuwa, gamida yanuwa da abokan arziki. Bayan shi an yi sauran nade-naden sarautar mutane biyar da sunka haɗa da Injiniyan noma, Engr. Jika Naino wanda aka naɗa Dangaladiman Gobir, Dankasuwar Dakoro Malam Ousmane Balla Na-Allah da aka naɗa Masarin Gobir, Dankasuwa a Boungugi Elhj Chaibou Oumarou da aka nada Barden Gobir, Mashari’anci(Advocate) a Birnin Yamai Malam Laouali Amadou Madougou shi kuma aka nadashi kadon Gobir, sai kuma Dankasuwa a Birnin Tsibiri Malam Abou Gonda da aka naɗa sarautar Dangaladiman Sarkin Fawan Gobir.

Sarautar Dan gara a Gobir, ta bakin Sani Danbieto Gobir, ma’anarta shine Sarki baya bada umarnin yaki sai da sa bakin Dan gara. A takaice sarautar dangara sauratace ta shawara kan harkokin da sunka shafi yaki a da.

Abdul Mailahiya Hausa

I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder and Operator at Bago Technologies. My hobbies are Reading, Travelling and Discovering.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post