Shugaba Buhari a Tahoua wajen halartar bikin 18 Dicemba a Nijar

Shugaban kasar Nijeriya, Shugaba Muhammadu Buhari zai halarci bikin cika Jamhoriyar Nijar shekaru 59 da samun jamhoriya daga turawan mulkin mallaka na Taransa. Taron wanda ake ran 18 ga watan Dicemba a ɗayan jahohin kasar. A wannan shekarar 2017, bikin ya faɗa a Jahar ta Tahoua inda tuni ake ta ma jahar kwaskwarima birni da karkara dan tarben maziyarta da nuna musu irin aikin da shugaban kasar yayi mai taken Tahoua sakola.

Babban mataimaki na musamman ga shugaban Kasa a harkokin yada labarai, Malam Garba Shehu, ya bayyana ziyarta cikin wata sanarwa da aka bayar a Abuja a yiya Lahadi, 17 ga watan Dicamba cewa shugaba Buhari tare da shugabannin Mali, Burkina Faso, Chadi, Mauritania da Nijar zasu halarci babban taron.

Shehu ya ce gwamnonin da zasu rakki shugaban sun hada da Gwamnan Katsina Aminu Masari, Gwamnan Yobe Ibrahim Gaidam da Gwamnan Maiduguri Shattima.

Abdul Mailahiya Hausa

I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder and Operator at Bago Technologies. My hobbies are Reading, Travelling and Discovering.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post