Hirar Fatima Ganduje da wata Jarida: Yanda soyayya ta hada ni da miji na

Fatima Ganduje diyace ga Gwamnan jahar Kano mai ci yanzu wadda akayi bikin aurenta da mijinta, ɗa ga Gwamnan jahar Oyo Idris Ajimobi a kwanakki. Shekarun Fatima 24 da haihuwa, ta kammala karatunta na jami’a da digiri mafi kima(first class) a jami’ar kasar Amurka dake jahar Adamawa (Abti). A cikin hirarsu da wata jarida Fatima ta bayyana yadda soyayya ta hadata da mijinta har sunka kai ga aure.

A wata tattaunawa da editan City People yayi da ita, Fatima ta amsa wasu daga cikin tambayoyin da ya mata kamar haka:

Da alama kina jin dadin rayuwar aurenki? Fatima ta amsa da cewa Eh, Tabbas hakane tun bayan da muka yi aure na kasance cikin farin ciki a gidan mijina.

Shin zaki iya gaya mana yanda kuka hadu?, ta amsa da cewa dogon labarine amma a takaice, mun hadune sanadiyar wani dan uwanmu, kuma muna haduwa muka shaku da juna.

Zaki iya gayamana kalmar farko da ya fara gayamiki lokacin da kuka hadu?, ta amsa da cewa, ya cemin zan iya sanin ko ke wacece, sai na amsa da cewa Eh, me zai hana.

Tsawon wane lokaci kuka dauka kuna soyayya?, shekara daya da kusan rabi.

Shin zaki iya gayamana wane irin mutum ne mijinki?, ta amsa da cewa mijina mutumin kirkine yana kula dani kuma dukkan abinda nake nema a tattare da miji yana dashi.

Shin yaya kike kina kwalliya ki fito da kyau haka, tsawon wane lokaci kike dauka kina kwalliya?, sai ta amsa da cewa bana wani dadewa mintuna talatin kawai sun isheni, saboda nasan abinda zansa ya min kyau.

Shin yaya zaki bayyana ‘yan uwan mijinki?, tace, suna son dan uwansu sosai kuma nima suna nunamin soyayya babu wani nuna banbanci.

Shin a matsayinki na bahaushiya yaya kikeji da kika auri bayerabe?, sai tace, Ni ba bahaushiya bace, ni bafulatanace.

Idan da ace bahaushe kika aura kina tunanin zaki samu babbanbancin soyayya?, sai tace ai soyayya ba ruwata da yare.

Kin iya yarabanci? , sai tace a’a nadai dan fara koyo(tayi wani yarabanci kadan) tace amma tana sa ran nan gaba zata iya sosai haddama abincin yarbawa duk tana so ta iya.

Ya zaki bayyana uwar mijinki?, tace mutumnjyar kirkice tana mun abinda ya kamata, bama uwar mijin bace uwatace.
Thenet.ng

Abdul Mailahiya Hausa

I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder and Operator at Bago Technologies. My hobbies are Reading, Travelling and Discovering.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post