An kama wani mutum da ke yi ma wani Senata sojan gona, ya na damfarar masu neman aiki a Facebook

A lokacin da aka kama shi, anyi zargin cewa ya damfari masu neman aiki ta ko halin ‘ka’ka makudan kudade. Joel, a Facebook ya bukaci kudi tsakanin N200,000 da N350,000 daga hannun masu neman aiki, sannan yayi masu alkawarin sama masu aiki a kamfanonin mai a kasar.

Amma dubunsa sun cika ne a ranar Litinin, bayan daya daga cikin wadanda suka shiga tarkonsa, Misis Chinelo Nwadin, wacce ya wanka ta kai kara ga kwamishinan yan sanda a jihar Lagas, Mista Imohimi Edal, inda ta sanar dashi ayyukan sa.

An kama wani mutumi dake yiwa wani sanata sojan gona yana damfarar masu neman aiki a Facebook

Mai karar tayi zargin cewa mai laifin ya karbi N300,000 daga hannunta ba tare day a bata ko wani aiki ba kamar yadda yayi alkawari.

Edgal ne ya uurci mataimakin kwamishinan yan sanda na Area D Mushin, Mista Olusoji Akinbajo da ya kamo mai laifin.

Kakakin yan sandan jihar Lagas, Chike Oti, wanda ya tabbatar da kamun yace ana nan ana cigaba da bincike.

Abdul Mailahiya Hausa

I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder and Operator at Bago Technologies. My hobbies are Reading, Travelling and Discovering.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post