Yau ta ke Jajibirin Sallah Ƙarama a Jamhoriyar Nijar

Kamar yadda ya bayyana a hoto, duk Ranar Jajibirin Bikin Sallah a Maradi Iyalai na gangama su sayi Bisashe wanda zasu yanka gwalgwadon hali, inda shi kuma Sarkin Gari ake kawo mishi Gawurtaccen Sa wanda zai yanka yai nashi shagalin bayan an gama Wasan Hawan Kaho da an taso Idi.

Bayan shafe kwanakki 29 ana azumtar watan Ramadan farkon ganin wata a Jamhoriyar Nijar gami da wasu kasashe na yamma ga Nahiyar Afrika irinsu Ivory coast da Mali yau Laraba suke fara dibin jinjirin watan Shawwal wanda bayyanarshi ke nuni da karshen watan Ramadan. Da zarar ya bayyana yau to gobe Alhamis 14 ga watan Yuni take Sallah Karama.

Tuni Mutanen Jahar Maradi suke ta shirye-shiryen tarben shagalin Bikin Sallar Karama. Allah yasa a gama lafiya.

Abdul Mailahiya Hausa

I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder and Operator at Bago Technologies. My hobbies are Reading, Travelling and Discovering.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post