Wani ɗan ƙuru ya yanke Mazakutar shi saboda cuta

Hausawa sunce inda ranka ka sha kallo. Yayinda dubban mazaje a fadin duniya ke ta faɗi tashi dan ƙoƙarin inganta nasu, yau ga wani ɗan ƙuru daga kasar Rasha mai suna Adam Curlykale ya kai kanshi Asibiti da gan-gan inda ya biya likitoci kudi suka yankemai Mazakutarshi da kan Nonuwanshi wai suna rage mai kyan jiki. Mutunen dai fari ne fat, amman saboda tsabar zanen da yake ma jikinshi “Tattoo “, ya koma baki wuluk.

An tabbatar da cewa kashi tasa’in cikin dari na jikinshi duk zanen “Tattoos” ne, ya kwashe shekaru 12 yana ma jikinshi wannan zanen ta yanda har gaba dayan jikin nashi, hadda Idanu sun koma bakake, ya bayyana cewa gabanshi da maraina da nonuwa da ya bukaci a yankemai suna bata mishi zanen jikin nashine shi yassa ya yanke shawarar cewa be da bukatar su.

Mutumin dan shekaru 32 ya tafi har kasar Mexico inda a canne aka mai wannan aiki.

Daily Mail ta ruwaito cewa, bayan kammala cirewa Adam sassan jikin nashi ya gayawa manema labarai cewa shi ya san shi na dabanne a cikin mutane dan haka ya dena damun kanshi da tunanin me zai faru gobe, rayuwa bata da tabbas dan haka mutum yayi abinda yake son yi ba tare da jinkiri ba,injishi.

Abdul Mailahiya Hausa

I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder and Operator at Bago Technologies. My hobbies are Reading, Travelling and Discovering.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post