Kamannin Wani Zabaya da Matar shi Baƙa Wuluk sun ɗauki Hankulan Mutane

Ƙasar Kamaru na daga kasashen da ke da mafi yawan zabaya a Nahiyar Afrika, ko da ya ke a kwanan baya mun samu labari cewa wasu Bokaye na amfani da sassan jikin su wajen hada Asirin Kudi da saraun su wanda ya cusa wasu baragurbin mutane farautar su su na hallaka su ba su ji ba su gani ba. Waɗanga kamannan da mun ka kawo muku yau na wani Zabaya ne ɗan Kamaru da shi da Matar shi baƙa da babu irin ta wadda mu ke ganin Yar Asalin Sudan-ta-Kudu ce.

Kamannan sun ɗauki hankula matuƙa a kafofin sada zumunta. Sun haska kamannan rungume da ɗiyar su, ita ma ta burge sosai!

Masharhanta sun yi ta tofa albarkacin bakin su danganeda launin fatar wannan mata wadda mu ke ganin za ta iya lashe Gasar Sarauniyar kyau a Afrika.

Ragowar kamannai:

Abdul Mailahiya Hausa

I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder and Operator at Bago Technologies. My hobbies are Reading, Travelling and Discovering.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post