Sakamakon Zaɓen 2019: Wani Gwamna ya fito fili ya bayyana yanda Atiku ya lashe takarar Shugaban ƙasa

Yayinda sakamakon zaben fidda na takarar Shugaban kasa karkashin Jam’iya mai adawa PDP ya ba kowa mamaki, Wani Gwamnan a Arewacin Nijeriya ya fito fili ya bayyana abubuwanda sunka sa Tsohon Shugaban kasa, Atiku Abubakar ya lashe wannan takarar, ya doke yan takara irinsu Tsohon Gwamnan Kano Kwankwaso, Tambuwal, Dankwambo dss. Gwamnan Jahar Taraba, Darius Dickson Ishaku, ta bakin mai magana da yawunshi, Bala Dan Abu ya bayyana cewa, so da kuma jajircewar Atiku wajan ganin ya bautawa kasarshi su sunka kai shi ga nasarar lashe zaben fidda gwanin na Jam’iyar PDP. Ya kuma yaba da yadda aka gudanar da zaben cikin ruwan sanyi, tsari da nuna kishin kasa. Haka kuma ya yaba da yadda sauran ‘yan takara saboda halin dattakon da sunka nuna.

A karshe yace nasara na tare da jam’iyyarsu ta PDP a zabe mai zuwa.

Abdul Mailahiya Hausa

I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder and Operator at Bago Technologies. My hobbies are Reading, Travelling and Discovering.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post