Zaɓen 2019: Saraki da Atiku na ƙulla-ƙulla a Dubai dan gano yanda PDP za ta kada Buhari

Dan takarar shugabancin kasa a jam’iyar adawa ta P.D.P Atiku Abubakar tare da kakakin majalisar dattawa Bukola Saraki Da Kuma Shugaban P.D.P na kasa Prince Uche Secondus suna zaman tattaunawa a hadaddiyar Daular Larabawa U.A.E Dubai dan gano yadda zasu kada Shugaba Muhammadu Buhari a zaben 2019. Tattaunawar ta kara hadawa da wasu masu ruwa da tsaki na jam’iyar P.D.P wadanda sunka hada da tsohon Gwamnan Anambra, Mr Peter Obi wanda kuma shine zai marawa Atiku baya a takarar Shugabancin kasa sai kuma Shugaban tsare-tsare na takarar Atiku wato tsohon Gwamnan Ogun Gbenga Daniel wadanda tuni sun isa Dubai din ne a daren Laraba, 24 ga Oktoba.

Kana kuma tattaunawar zata kara maida hankali ta yadda za’a fuskanci gangamin zabe wanda tuni hukumar zabe mai zaman kanta wato Inec ta sanar da jadawalin fara gangami wanda za’a fara na Shugaban kasa da yan Majalissun tarayya dana dattawa a 18 ga Nuwamba, sai kuma na Gwamnoni a 1 ga watan Disamba.

Abdul Mailahiya Hausa

I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder and Operator at Bago Technologies. My hobbies are Reading, Travelling and Discovering.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post