A Kano Wani Ɗan Tsibbo zai sha darmun Shekaru a Gidan Yari

Wani mutum mai suna Abubakar Ishak da aka fi sani da Mairakumi a Jahar Kano zai sha daurin shekara 10 a Gidan kaso, bayan Kotu ta kama shi da laifin rike jabun kudin Dalar Amurka guda 176. Hukumar dake yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa ta’annati, wato EFCC ce ta gurfanar da Abubakar Ishak Mairakumi a gaban babbar kotun tarayya da ke Kano. Kotun karkashin jagorancin mai shari’a Lewis Allagoa, ta tuhumeshi da aikata laifuka biyu, ciki har da mallakar kudin jabu na takardun dalar Amurka guda 176.

Abdul Mailahiya Hausa

I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder and Operator at Bago Technologies. My hobbies are Reading, Travelling and Discovering.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post