Dalilan da sun ka sa Mataimakin Gwamnan Jahar Sokoto ya yi Murabus

Jiya Laraba 14 ga watan Nuwamba Maigirma Mataimakin Gwamnan Jahar Sakkwato Alh. Ahmad Aliyu Sokoto ya aika ma majalisar dokokin Jaha wata takarda ɗauke da bayanin ya yi murabus daga matsayin shi na Mataimakin Gwamna. Wannan dai ya zo ne a na gab da gangamin fara neman zaɓe.

Ahmad Aliyu dai tuni ya ki bin Gwamnan Jahar Hon Aminu Waziri Tambuwal bayan ya sauya sheƙa daga Jam’iyya mai Mulki ta A.P.C ya koma Jam’iyyar adawa ta P.D.P a ƙoƙarin shi na ganin ya samu tikitin tsayawa takarar Shugaban kasa a jam’iyyar P.D.P abunda ya ci tura inda ya zo na biyu a zaɓen fidda gwanin da Atiku Abubakar ya samu damar samun tikitin tsayawa takarar, shi kuma ya zo na biyu.

Sakamakon hakan dai jam’iyyar A.P.C ta kyautata ma Ahmad Aliyu ta tsaida shi takarar gwamna wanda a na sa ran zai kara da ubangidan shi a zaɓe mai zuwa muddin P.D.P ta sauya dan takarar gwamnan ta kamar yanda a ke zato wanda yanzu haka Munir Dan’iya ne ke yin takarar kafin a sauya shi da gwamna mai ci wanda dama abokin shi ne.

Abdul Mailahiya Hausa

I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder and Operator at Bago Technologies. My hobbies are Reading, Travelling and Discovering.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post