Sarauniyar kyau a Sudan ta kudu ta sa Sadaki da tsada

Mazaje a Sudan-ta-kudu sunyi caa ga wata Santaleliyar Budurwa yayinda ta hauda hotunanta a Facebook tana neman mijin aure a sadaki mai tsada Dalar Amurka $10,000, Shanu 530, Motoci samfurin V8 guda 3. Matashiyar Nyalong Ngong Deng Jalang (A hannun dama a hoton
labari) mai shekaru 16 da haihuwa yanzu haka akwai maza biyar da ke ci gaba da gogayya da juna dan neman aurenta.

Tashar rediyon Sudan ta Kudu, Tamazuj ta sanar da cewa, a sahun wadanda ke kai kon dan samun amincewarta da wani sanannen kusa na gwamnatin kasar. Tuni matasa daga sassa dabam-dabam na cikin wajen kasar Sudan ta Kudu ke cigaba da cincirindo a kafar Facebook dan gwada sa’arsu wajen daukar wannan allurar cikin ruwa, inji su.

Abdul Mailahiya Hausa

I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder and Operator at Bago Technologies. My hobbies are Reading, Travelling and Discovering.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post