Taron Naɗin Sarautar Wazirin Hausa Alh Yakubu Gobir a Garin Daura (Photos)

A Jiya Talata an ka yi Wankan Sarautar Alhaji Yakubu Gobir a Daura, Jahar Katsina wanda yan uwa da abokan arziki daga bangarori dabam-dabam na Nijeriya da Makwabta sun ka halarta. Alhaji Yakubu Gobir Matashin Dan Kasuwa ne, Maitaimakawa Gajiyayyu, kana kuma Jigo ga tafiyar Jamiyyar APC A Jahar Kwara. Shine ya sayo Motoci dari biyu (200) ya bada dan yakin neman Zaben Shugaba Buhari da Mataimaki Osinbajo.

Maimartaba Sarkin Daura, Dr. Alhaji Umar Farouk ya nada mai Sarautar Wazirin Hausa ganin irin taimakon da yake a Jahar Kwara da sauran Jahohi a Arewacin Nijeriya. Sardaunan Gobir, Dr. Ibrahim Abdullahi Gobir tareda tawagarshi sun halarci wannan wankan sarauta a Garin Daura. Allah ya taya Waziri riko.

Ga Ragowar Kamannai daga Taron nadin sarautar:
Abdul Mailahiya Hausa

I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder and Operator at Bago Technologies. My hobbies are Reading, Travelling and Discovering.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post