Zaɓen 2019: Motocin yaƙin neman zaɓen Shugaban kasa sun bada mamaki a Legos

A Nijeriya ana ta shirye-shiryen tarben zaben badi 2019 inda za’a fara yakin neman zabe banda-gobe, wato ranar Lahadi mai zuwa. Tuni yan siyasa ke ta dada dubaru dan tunkarar zaben, jiya Alhamis ma an hango wasu Motocin basbas kirar Hyundai manne da sunan “Gobir Organisation” bisa hanyar Legas zuwa Ibadan su kimanin 100 wanda duk an musu zane da hotunan Shugaban kasa, Muhammadu Buhari. Motocin sun cika kan titi inda Yarabawa sunka taru suna kallon abun mamaki, kamar yadda shafin Autojosh ya ruwaito.

Sabuwar motar bas din ta Hyundai H1 2009 ana saida ita kan farashin Naira miliyan 7. Sannan kuma ana samun ta hannunta tsakanin Miliyan 2.5 zuwa miliyan 3.

Ga hotunan Motocin bisa hanyarsu ta tafiya:
Abdul Mailahiya Hausa

I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder and Operator at Bago Technologies. My hobbies are Reading, Travelling and Discovering.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post