Shin wace kiɗa ce za ta dace da Matashin ɗan Kwallon da Real Madrid ke so Brahim Diaz?

Da yawa daga cikin magoya bayan Real Madrid sukanyi mamakin miyasa Madrid ke bukatar sayo matashin dan wasan gaban Manchester City Brahim Diaz.
abunda basu saniba shine Diaz nada kwarewa a mafi yawancin lambobi kamar lamba 10 ganin irin yadda yake iya rike kwallo da kuma bayarwa wanda hakan zaisa yayi gogewa da Luka Modric,Dani Ceballos sai kuma dan wasan gaba na gefe inda ya kasance dan wasa mai matukar sauri wanda ya kware wajen yanka wanda hakan yasa zai fuskanci gogewa da yan wasa kamar Lucas Vasquez, Isco, Marco Asensio da kuma Gareth Bale bugu da kari kuma Diaz zai iya buga dan wasan gaba na tsakiya wato lamba 9 wanda hakan yasa zai zamewa Benzema da mariano barazana a takaice dai zuwan Brahim Diaz a Real Madrid zai kara rura wutar gogewa da kuma gasa tsakanin lambobin da yawa daga cikin yan wasa wanda yanzu hakama Isco da Marco Asensio suke ta kokarin ganin sun samu shiga cikin yan wasa 11 na farko A Real Madrid inda shima matashi Vinicius Junior baya samun wani isasshen lokaci.

Abdul Mailahiya Hausa

I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder and Operator at Bago Technologies. My hobbies are Reading, Travelling and Discovering.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post