Tsarin da Gwamna Tambuwal ya kawo na rashin amfani da 'yan Bangar Siyasa Sokoto alheri ne ga Matasa

A Duk kowane zabe dayake gudana a Nigeria ana kara samun baragurbin yan siyasar dake gurbata goben yawancin matasa ta hanyar cika musu ido da kudi ko basu kwayar da zata gusar musu da hankali, wanda yakan jawo kara susucewar tarbiyar matasa,zaman banza ta’ddanci da kuma kara samun matasa cima kwance a cikin al’umma.
kwatsam sai gashi a wani tsari da mai girma gwamnan jahar Sokoto Hon Aminu Waziri Tambuwal yazo dashi ana samun raguwar wannan bala’i dake faruwa a cikin al’umma, ta hanyar dakile duk wata hanya ta amfani da matasa don farmakar abokan gaba ko bangar siyasa a lokacin yakin neman zabe wanda hakan yasa yanzu wasu da dama sun fara gano inda aka nufa wanda ana zaton cewa muddin sauran yan siyasa sukayi koyi da irin wannan salo na gwamna Tambuwal to ayyukan ta’addanci zasu ragu a Nigeria wanda dama can yawanci yan ta’adda tsohin yan bangar siyasa ne da uwayen gidansu ke watsi dasu da zarar an kammala zabe bayan su nisantar dasu daga hanyar neman na halali ko kuma na guminsu sai dai a dauka a basu.

Abdul Mailahiya Hausa

I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder and Operator at Bago Technologies. My hobbies are Reading, Travelling and Discovering.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post