Son Taimakon Talakkawa ne ya sa ni tsayawa Takara Karo na Ukku – Hon Yusuf Muhammad

Dan majalisar Jaha mai wakiltar Sabon Birni ta Arewa Hon Yusuf Muhammad Gobir a lokacin da yake ganawa da wani bangare na jama’ar da yake wakilta ya sake jaddada ma al’umma dalilin da yassa ya sake yanke hukuncin tsayawa takara, inda yake shaida masu cewa son da yakema talakawa ne ya sashi sake tsayawa takara wanda wasu lokkuta da sunka shude anyi ta yaudarar talakawa musamman mutanen karkara inda zakaga da zarar an kammala zabe basu sake ganin wakilin su sai wani zabe ya sake zagayowa, amman shi a shirye yake ya kara lumka irin ayyukan da yake yi masu musamman bangaren ruwan sha wanda a baya rashin samun tsabtataccen ruwan sha ya zama barazana ga sama da kashi 30 na lafiyar yaran da ake haihuwa, inda da yawa sukan tashi a matsayin guramu ko kuma da shanyayyen jiki.

Hon Yusuf ya kara da cewa kuma a bangaren mata zaya sake lumka kokarin da yakeyi ta hanyar kara tallafama mata da jari domin dogaro da kansu musamman wadnda mazajen su sunka rasu da kuma sake tallafama yara mata yan makaranta masu koyon likitanci.

Allah ya cika nufi”

Abdul Mailahiya Hausa

I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder and Operator at Bago Technologies. My hobbies are Reading, Travelling and Discovering.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post