Ashe Alu ya san da cewa mutanen Isa da Sabon Birni Bello Shehu Sulaiman su ke so?

A ranar Attanin Jam’iyyar APC ta gudanar da gangamin yaƙin neman zaben ta a karamar hukumar mulki ta Sabon Birini inda wani abu da bai yi ma manya-manyan jigogin jam’iyyar tare da magoya bayan su dadi ba, ya sake bayyana na irin tarbar da halastaccen ɗan takarar dan majalisar wakilai na Isa/Sabon Birni ya samu wato Bello Shehu Suleman wanda shine wanda yayi nasara a zaben cikin gida da aka gudanar amman daga karshe aka musanya sunanshi da dan majalisa mai ci yanzu wato Engr Aminu Sani Isa wanda ana tunanin an maida mishi da takara ne saboda kin sauya shekar da yayi zuwa jam’iyar PDP duk da irin tarin goyon bayan da matashin dan siyasar wato Bello Shehu Suleman ya samu.

Sai dai jigon jam’iyar ta APC a jahar Sokoto wato sanata Aliyu Magatakarda Wamakko ya jinjina ma Bello da jama’a na irin biyayyar da yayi na bin hukumcin manya-manyan uwayen jam’iya inda ya kwatanta shi da mutun mai kamun kai da rikon amana sannan kuma ya kara kira ga jama’a da su rike dan su da hannu biyu-biyu.

Yayi kyau.

Abdul Mailahiya Hausa

I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder and Operator at Bago Technologies. My hobbies are Reading, Travelling and Discovering.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post