Shisha na matuƙar cutarwa ga Lafiyar Jikin ku fiye da Sigari, ta bakin Manazarta Kimiya

Ba shakka Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta dauki kwaƙƙwaran mataki a bara, Yuni 2018, dan hana Matasan Nijeriya shan Shisha amman duk da haka, ba su hanu ba. Na ga aboki na na yi shi ke sa kashi 60% cikin 100% mutane shan Shisha, haka abun ya ke ga Mashaya Tabar sigari ita ma. Amman ka san cewa Shisha na da aibu ga lafiyar jikin ka fiyeda Taba- ta fi saurin kashewa da Sigari din!

Manazarta kimiya a Sharjah da Abu Dhabi sun gano cewa Shisha nada matukar matsala ga lafiya in aka kwatamtata da Tabar Sigari. Ta bakin NAN, Malama Ayesha Mohammed, Malamar dake koyarda Kyemistiri a Jami’ar Sharjah da jigon binciken sun tabbatarda cewa: “Tabar Gargajiya (Medwakh) da Shisha basuda matata. “Dan haka gurbatattun sinadarai zasu iya shiga salkar huhu, su haifarda cutukka dabam-dabam, kamar sankarar huhu da baki, cutocin baki da toshewar magudanar jini. “Bani shawartarku ga shan Dokha (Medwakh) da Shisha don basuda matata, don haka tarkacen sinadarai zasu iya shiga cikin jikin mutum su haifarda illa in aka kwatamta da Sigari su kuma haddasa sankarori dabam-dabam.”

An wallafa a shafin binciken ilimin Toxicology dake Jami’ar Oxford, binciken na baya-bayan nan ya maida kai a kayan hadin Tabar Medwakh 13 da kayan hadin Shisha ukku, aka nazarta kayan hadin dan gano wanda sinadaranshi ya rinjaya.
An auna mizaninsu da na Tabar Sigari dan gano wadda keda tsantsar illa ga lafiyar jikin mutum. Sinadarin nickel, sanannen sinadari (carcinogen) dake cikin Medwakh da Shisha ya fiye yawa in aka kwatamta da wanda ke cikin Tabar Sigari, yayinda aka gano cewa mizanin sinadarin iron ya zo kusan daidai.

Wanda sunka gabatarda binciken sune Prof. Mohamed Al Hajjaj na Jami’ar Sharjah; Abdus Khan na Jami’ar Khalifa, Abu Dhabi; da Shabber Mohammed da Masrath Mohammed, duk a Jami’ar Jazan, Saudi Arabia.

Farkon wannan shekarar, Malama Mohammed da wasu abokan bincike sun bayyana wani aiki da ya bada rahoton cewa akwai yawancin mizanin sinadarin nicotine da tar a Medwakh fiyeda na Sigari, yayinda na shisha da sigari sunka zo kusan daya.

Dr Noordin Wadhvaniya, wani Kwararren Likitan shed’a a Asibitin Kanada ta Musamman dake Dubai, yace mutanen dake shan hayakin
shisha na shakar adadin sinadarin uranium so 26. “In aka yi wani dubi,
uranium da kuke shaka zai iya lalata kododin mutum, ba ma huhu ba. “Hakazalika, yana lalata masheda, haifarda radadin sheda da shanyewar maikon ruwan huhu, bisa kari,” yacce.

Wadhvaniya ya kara da cewa shaka daya ta Tabar shisha, kamar mashayi ya shanye hayakin karen Sigari daya ne. Tambaya a nan ita ce, mi yassa matasa sunka dage ga shan Shisha har ma Sigari? Watsa wannan bayanin ga abokai da yanuwa. Sunada bukatar sanin wannan.

Abdul Mailahiya Hausa

I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder and Operator at Bago Technologies. My hobbies are Reading, Travelling and Discovering.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post