Ƙuri'ar mu ƴancin mu; Kar mu yarda mu saida goben mu

Tabbas lokaci dole a jira shi a yau lokacin da kowa yake jira gashi yazo wato zaben game gari da zai gudana a shekarar 2019 sai dai wani kalubale ga talakawa wato dole a wannan karo a gusad da kwadai ko son abun duniya kasancewar da yawa daga cikin ‘yan siyasa sun maida talakawa karnukan farauta da basuda wani amfani garesu sai lokaci irin wannan wanda da yawa daga cikin su da zarar sunci zabe su da talakawa sai dai daga hannu.

Basu kula da wani bukatun al’ummar da suka zabesu sai dai yawancin talakawa sukan yi saurin mance irin wannan hali na yan siyasa saboda wata dubara da suke amfani da ita idan zabe ya karato wato bi gida gida tsakanin kauye da Birni suna raba ma masu zabe kudi, kudin da zasu kare ba tare da wanda akaba yayi wani muhimmin abu da su ba, amman haka zaka ga akan ma wannan yan kudi jama’a sunata mantawa da inda aka fito duk da cewa koda ka karbi kudin dan siyasa bayada wani karfi da zai tabbatar da sai ka zabeshi.

Don haka talakawa mu tsaya mu tantance wadanda yakamata mu dankama amanar mu.

Abdul Mailahiya Hausa

I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder and Operator at Bago Technologies. My hobbies are Reading, Travelling and Discovering.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post