Abba Kabir Yusuf ya zama dan gata, Lauyoyi 100 zasu tsaya mai kan zaben Kano

Abba Kabir Yusuf wanda aka fi sani da “Abba gida gida” ya zama Dan Gata biyo bayan sakamakon zaben Kano wanda ya gudana satin da ya gabata. Abba wanda ya tsaya takarar kujerar Gwamnan Kano karkashin Jami’iyar PDP, ya ga samu, ya ga rashi, amman karshe akwai fatan nasara gareshi.

Bayan an kammala zaben farko na Gwamnoni wanda ya gudana a Nijeriya ranar 9 ga watan Maris na 2019,sakamako ya bada cewar Abba ne ya ci zabe inda ya doke Gwamna mai ci Dr. Umar Abdullahi Ganduje da kuri’u masu yawa, INEC ta sanarda sakamako, yan Kwankwasiyya mutanen Tsohon Gwamna Rabi’u Musa Kwankwaso, harda Adam A Zango da Mustapha Naburuskka da Naziru Ahmad Sarkin Waka dss sunka buge da murna nasu yaci zabe. Kawai kwatsam sai kuma akace zaben bai kammalu ba saboda wasu dalilai- sai an sake maimata zaben wasu yankunan Birnin Kano da na Kauyukka. Wasu Gwamnonin Arewa da wasu Malamai sun fito fili sun bayyana rashin amincewa da sakamakon na hukumar zabe mai zaman kanta INEC.

Aka maimaita ran Assabar 23 ga Maris a wasu sassan Kano. Sati ya kewayo akai zabe, amman wanga karon ba kamar na satin baya ba wanda akai cikin lumana da kwanciyar hankali inda Kanawa sunka fito kwansu da kwarkwatarsu sunka kada kuri’su daya bayan daya ga yan takarar da suke so. Mutan Kano sun kai kokensu ga Shugaba Muhammadu Buhari wanda tuni yan bar masu kasar zuwa Kasa mai Tsarki Saudi Arabia don gudun ko kar a zargeshi. Sun yi koken cewa zaben bai yi ba saboda kazamin rikikkan da aka yi ranar maimaita zaben. Wanga bai hana Hukumar INEC sanarda sakamakon zaben ba, karshe ta sanarda cewa Ganduje ne yaci zaben.

Nan ma mutane Kano da ma wanda ba na Kano ba, wato yan sa ido, sun nuna rashin gamsuwa da sakamakon saboda zaben ba’a yishi bisa tafarkin demokradiya ba. Mun samu labarin cewa ma anyi kashe-kashen rayukka ranar maimaita zaben, an jima Bayun Allah rauni, an hana wasu yan jam’iya fitowa suyi zabe…

Wadanna dalilai da ma wasu sune sunka tursasa Lauyoyi Samada Guda Dari 100 yanzu haka a fadin Nijeriya,
karkashin jagorancin Audu Bulama Bukarti daukar alkawarin
kwatoma Abba hakinshi a Kotu ba tareda ya biya ko sisin kwabo
ba. Cewar Lauyoyin zasu yi haka ne domin kare Martaba da
kimar Dimokradiyya da wasu ke amfani da ita wajen
kwantatama wasu mutane.

Allah ya bada sa’a. Ameen.

Abdul Mailahiya Hausa

I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder and Operator at Bago Technologies. My hobbies are Reading, Travelling and Discovering.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post