Makomar Tsadaddar Tsintsiyar APC a Birnin Abuja

Hotunan Tsadaddar Tsintsiyar da taci makuddan kudade wadda Jam’iyar APC ta sa aka kafa mata a kofar shiga Birnin Tarayya Abuja. Tun farkon yakin neman zaben Shugaban kasa, Sanatoci da Yan Majalissu aka fara kafa wannan Tsintsiyar mafi girma a Duniya wadda alamace ta Jam’iyar mai mulkin Nijeriya. Kun ga yanda wannan Tsintsiyar da ta kafa tarihi ta zama yanzu? An kashe maƙuddan kudade wajen ginata amman yau ba zaku so ku ga makomar wannan Tsintsiyar ba saboda rashin kula da sakaci.

Katuwar Tsintsiyar da ta lakume makuddan kudade har Naira Miliyan Dari biyu da hamsin(N250 milion naira) ta gamu da hushin wasu yan adawa inda sunka tunkudeta, sunka bar karfuna dake tangale da ita.

Kudin sun bi iska kenan. Wai har Miliyan 250 na naira!

Abdul Mailahiya Hausa

I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder and Operator at Bago Technologies. My hobbies are Reading, Travelling and Discovering.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post