Micece ribar ku da ke son ganin rushewar siyasar Senator Ibrahim Abdullahi Gobir?

Hausawa na cewa da garin wasu gwamma garin ku, kuma naka shine naka.

A wani al’amari da yawa wasu Gobirawa sunka manta shine tun zamanin BABARI daya shuɗe Gobirawa sunka zama yan rakkiya ta bangaren siyasa a Jahar Sakkwato na rashin wani jigo ko wani mai karfin fada aji wanda hakan yassa ko’ina mukaman siyasa baka ganin an ba dan ainahin Gobir wani matsayi daya kai a faɗa.

Amman lokaci guda sai gashi Allah ya turo da wani Da da ya share muna hawaye wato Engr Dr. Ibrahim Abdullahi Gobir Mfr, Sardaunan Gobir, wanda kafin zuwanshi mutane da yawa basu san amfanin wani Sanata da yake wakiltarsu ba. Tun hawanshi matsayin sanata darajar Gobirawa ta fara farfadowa bama bakin Jahar Sakkwato ba, a’a duk fadin Nijeriya da Afrika baki dayanta. Amman sai kuma ana samun wasu daga cikin Gobirawan suna kokarin ganin duk wata tafiya tashi ta tsaya cik duk da cewa a halin yanzu babu jigo irinai a duk fadin Gobir.

Wanda da bukatar su ta biya da yanzu kuma a Gobir sake samun wani irinai sai wani lokaci da Ubangiji ne kadai ya sani.

Allah ya kara ɗaga Senator Dr. Ibrahim Abdullahi Gobir da ma Gobirawa baki ɗaya.

Abdul Mailahiya Hausa

I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder and Operator at Bago Technologies. My hobbies are Reading, Travelling and Discovering.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post