Surukai: Tsoho Ganduje da Ajimobi kowane ya sha kaye a zaɓe – kun san laifin su?

Zaben Nijeriya na wagga shekarar 2019 ya tada ƙura ganin yanda salon Mukin Demokradiya ya cigaba cikinshi. Abubuwanda baka taɓa tsammani sun faru a wannan zabe, saɓanin Gwamnatin da ta gabata; an nuna yancin kai, an nuna kishin ƙasa, an yaki cin hanci da rashawa, sannan kuma an zabi cancanta. Alamace ta nuna cewa Nijeriya ta cigaba ta fuskar Demokradiya.

Yan ƙasa sun zabi waɗanda sunka ga sun dace su shugabancesu a gurabun mulki dabam-dabam. Farko wanda ya dauki hankali shine zaben Shugaba da na Sanatoci wanda ya gudana ran 23 ga watan Fabrairu inda yan kasa sunka fito kwansu da kwarkwatarsu sunka kaɗama Shugaba Buhari don zarcewa a Shugabancin kasar karo na biyu. Kasashen duniya da sunka cigaba da masu sa ido sun yaba da yanda aka gudanarda zaben lami lafiya sannan kuma aka sanarda wanda ya ci zaben cikin kwanciyar hankali. Bayan na shugaban kasa, ran 9 ga Maris anyi na Gwamnoni da Yan Majalissu, shima ya kayatar sosai don yan kasa nan ma sun nuna kishin kai da zaben cancanta ba Jam’iya ba. Cikin Jahohin da aka yi zabe, akwai Kaduna, Benue, Taraba, Kano, Sokoto, Abia, Enugu, Oyo dss Cikinsu kab Zaben Jahar Kano ya fi daukar hankalin mutane saboda irin yakin da Yan Jahar sunka ɗaura damarar yi da abunda sunka kira cin amanar Jaha da Gwamnan mai ci yai masu.

Zaben na Kano ya kai kwana biyu ana tattara sakamakon zabe karshe aka sanarda Abba Yusif dan Kwankwasiyya na Jamiyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben. Ya kada Tsohon Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje na Jam’iyar APC da kuri’u da dama, duk da ana raɗe-raɗin Hukumar zabe INEC zata sanarda cewa zaben bai kammalu ba kamar yanda ta sanarda na wasu k.m.r Plateau, Adamawa, Sokoto, Benue, Bauchi da Cross Rivers. Zaben Kano bayyane yake ya kammalu. Sai dai in munaƙisa su ma ake so a shirya masu.

Shi kuma Surukin Ganduje wanda Danshi ya auri Diyar Gamduje, Gwamna Isiaka Abiola Ajimobi na Jahar Oyo shima ya sha kaye a zaben Sanatoci da aka yi a Jahar inda ya nemi takarar Sanatar Ibadan ta Kudu karkashin Jam’iyar APC. Dr. Kola Balogun na Jam’iyar PDP ya kada shi da kuri’u dubu sha-ukku da dari daya da arba’in da daya(13,141).

Babban laifin Tsohon Gwamna Abdullahi Ganduje shine wannan cin hancin da ya karba daga hannun yan wangila wanda Danjarida Jafar Jafar na Daily Nigerian ya tona asiri cikin bidiyoyi inda Ganduje yake amsar daloli yana sawa aljihu wanda labarin yayi ta yawo a kafofin janar gizo da dama. Sannan kuma wasu suna cewa baya kishin Jahar da Addinin Musulumci. Na tambaya to mi yassa ake kiranshi “Khadimul Islam”, an ka ce duk tusshiyace- a baki ne, ba a zucciya ba. Wato kenan har Kambun Yabon da Masarautar Saudiya ta bashi wanda GobirMob da kanta ta tayashi murna shima kenan yanda Jaki ya ga Jaka ne. Allah ya saukake.

Shi Surukin Ganduje, Tsohon Gwamna Abiola Ajimobi shi laifinshi shine rashin ɗa’a da girmama yan Jahar da ya bar yi daga baya, da sukar talakawa, duk da cewa Talakawan na Oyo sun ma shi uzuri har sunka zabeshi karo na biyu, ya shugabancesu Shekara takwas(8). Shine da wa’adinshi ya kare yace zai nemi Matsayin Sanata, nan Yarabawan Oyo na Oyo ta Kudu sunka ce zo kayi mu gani. Ya shafa ma Jam’iyar APC bakin jini ko Sanata bata samu ba balle Gwamna.

Har Madugun tafiyar Jam’iyar APC, Bola Ahmed Adekunle Tinubu ya mai gargadi ya bar biyarsu yawon neman zabe don kar ya shafa masu kashin kaji da Jam’iyarsu APC. Haka ko ta faru, ya shafa ma APC kashin kaji a Oyo!

Abdul Mailahiya Hausa

I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder and Operator at Bago Technologies. My hobbies are Reading, Travelling and Discovering.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post