Yaushe na za'a cimma karshen ta'addancin da a ke ma mutanen Zamfara?

Sannu sannu dai lokaci sai kara tafiya yake amman har yanzu bala’in dake matukar cima mutanen Jahar Zamfara tuwo a kwarya sai kara ta’azzara yakai. Wato al’amarin yin garkuwa da mutane tare da yima alumma kashin babu dalili abun babu alamun tsayawa duk da ikirarin da gwamnati kayi na cewa tana yin iyakar kokarin ta na ganin cewa an shawo kan wannan matsala.

Jahar Zamfara dai tayi zarra a bangaren noma amman a halin yanzu sai gashi alumma da dama daga yankin suna cikin wani hali na neman abunda zasu saka a bakinsu sabida fargaba ko gonaki a wasu wuraren ba’a iya nomawa amman duk da haka wasu al’umma da dama sun ja sun yi shuru duk da kuma Allah ya hore masu abunda zasu iya taimakawa dashi walau ta bangaren tsaro ne ko ciyarda wadanda sunka rasa mafaka.

Fatan mu dai Allah ya kawo muna zaman lafiya a Nijeriya dama duniya baki daya.

Abdul Mailahiya Hausa

I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder and Operator at Bago Technologies. My hobbies are Reading, Travelling and Discovering.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post