Dubun wani Sarki ta cika a Jahar Zamfara

Hukumomi na can suna bincike gameda wani Sarki a Jahar Zamfara sakamakon kamashi da hannu dumu-dumu a kashe-kashen dake abkuwa a Jahar bayan da Gwamnatin tarayya ta dauki kwakwararan mataki don daƙile kashe-kashen da garkuwa da mutane da ya addabi mutanen jahar da kewaye. A wata hira da wani sarki a jahar Zamfara yayi da daya daga cikin shuwagabannin ‘yan bindigar jahar ta bayyana inda aka ji suna tattaunawa akan cewa kawo jami’an tsaro Zamfara zai kara yawan zubar da jinine maimakon kawo karshen shi.

Jaridar Punch ta ce ta samu kwafin muryar da aka nada ta hirar sarkin da ba’a bayyana sunanshi ba amman ana tunanin yana yankin Zurmi ne na jahar ta Zamfara, anji sarkin da wani shugaban ‘yan bindigar na hira, Punch tace ta samu kwafin muryarne daga wata majiya daga hedikwatar soji.

A cikin muryar an ji shugaban ‘yan bindigar na cewa an kawo sojoji da ‘yan sanda sun kashe mai ‘yan uwa mata da ‘ya’ya, irin haka zubar jinine kawai zai kara sawa, yace yana bukatar sarkin ya rushe kungiyar ‘yan sa kai na kato da gora sannan ya zauna da manyan mutane a yankin a samu hanyar maslaha amma ba wai ta hanyar soji da ‘yansanda ba.

Yace harin da sojojin ke kawowa ta sama baya samunsu domin duk sanda jirgi zai kawo hari, kamin ya taso sun samu bayanin inda zai kai hari, dan haka suna barin wurin saidai su kashe tsuntsaye.

Ya kara da cewa, ko da sojojin kasa da ake aikowa kamin su zo sun san da zuwansu, dan haka suke shirya musu.

An ji sarkin na amsama shugaban ‘yan bindigar da hakane a maganganun da yake da kuma cewa suma basu goyi bayan kawo jami’an tsaro jahar ba sannan a akarshe ya amsa cewa zai rusa ‘yan kato da gora a yankin sannan zai zauna da manyan yankin da samo hanyar maslaha.

Hukumar tsaro dai ta zargi cewa akwai hannun wasu sarakuna a hare-haren na jahar Zamfara abunda sarakunan sunka karyata.

Abdul Mailahiya Hausa

I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder and Operator at Bago Technologies. My hobbies are Reading, Travelling and Discovering.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post