Kamannai: Ƴan China sun sha Wankan Rawunna Ranar Naɗin Sarauta a Kano

Jiya Alhamis ne an ka yi taron wankan sarautar wani Hamshaƙin Ɗankasuwa daga Ƙasar China wanda mun ka baku labarin shi kwanakkin baya. An yi wankan naɗin sarautar ne a Fadar Masarautar Kano.

An naɗa Mike Zhang a matsayin Waƙilin Ƴan Chanan Kano a Fadar Maimartaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu ranar Alhamis ɗin Ƴan Kasar Sin mazamna Jahar Kano, abokan kasuwa dss sun halarci wannan taro inda har wankan rawunnan sun ka yi, sun ka hau dawakai dan taya ɗanuwan nasu murna. Zak kyawo, ba laifi.

Ƙarshe Mike yayi jawabi cikin harshen Hausa inda yake cewa zai haɗa kan ƴan chanan kano dan kawo cigaban kasuwanci a Jahar wadda tun da daɗewa take tafiyarda ragamar kasuwanci a Kasar Hausa da ma Nijeriya baki daya.

Allah shi taya ka riƙo. Ameen.

Abdul Mailahiya Hausa

I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder and Operator at Bago Technologies. My hobbies are Reading, Travelling and Discovering.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post