Ko Shugaba Buhari bai ji dadin yanda Zaben Kano ya gudana ba

Bayan kammala Zaben Jahar Kano, wata kungiyar ‘yan jam’iyyar APC mai suna All Progressive Youth Forum ta rubuta takardar koke ga uwar jam’iyyar ta kasa domin yin bincike kan abubuwan da sunka faru a lokacin na Kano.
Kungiyar ta ce ta dauki wannan mataki ne ganin yanda goyon bayan da shugaban kasar ke samu a jahar yake samun koma-baya da kuma suka, saboda irin zarge-zarge na aikata ba daidai ba da sunka faru a zaben, wanda a bayanshi ne aka bayyana Gwamna Abdullahi Umar Ganduje a matsayin wanda yayi nasara.
Tuni dai jam’iyyar PDP wadda ta zo ta biyu a yawan kuri’u na Zaben Gwamnan ta yi watsi da sakamakon, kuma ta yi barazanar zuwa kotu, bisa abun da ta kira tayar da hankali, da kuma hana mutane kada kuri’a a lokacin zaben.
Daya daga cikin shugabannin kungiyar da ta rubuta wannan koke, Alwan Hassan ya yima BBC karin bayani, da cewa:
”Mu abun da muke son uwar jam’iyya tayi shine, a yi bincike a kan zaben cike-gibi da aka yi, a gano cewar; wanene ya shigo da mutane da sunka hana mutane zabe, suka rubuta sakamako?
Duk wanda aka kama da wannan magana jam’iyya ta hukumta shi, hukumcin korarshi daga jam’iyya.”
Alwan Hassan ya ce suna da cikakkun shedu na irin badakalar da wasu daga cikin jiga-jigan jam’iyyar tasu sunka yi a lokacin zaben, har ta kai ga samun nasara.

Dangane da maganar cewa, mi yasa a lokacin da ake magudin ba su dauki mataki ba, sai ya ce, ai su ba ‘yan sanda ba ne.
Saboda haka duk abun da za su yi, kawai shi ne sai dai su rubuta ma jam’iyya domin ta dauki mataki.

Kungiyar tace, tun lokacin da aka yi abubuwan da aka yi, ta ga ya dace ta zauna ta fitar da matsaya cewa, ita ba ta tare da abun da take cewa Gwamnan Jahar Abdullahi Umar ganduje yayi, saboda ya kayar da APC a Kano, kamar yanda ‘yan wannan bangare na jam’iyyar sunka ce.

‘Yan kungiyar sunka ce duk mutum mai hankali duk siyasarshi ba zai taba son abun da aka yi a kano ba, domin abun ya ma janyo ma Shugaban kasar zagi.

Masu koken sunka ce shugaban ya ki yin magana ne a kan lamarin saboda gudun kada a zarge shi da goyon bayan wani bangare.
A dalilin haka, ya zuba ido ga rundunar ‘yan sanda da hukumar zabe ta kasar a kan su yi abun da ya kamata kan lamarin.

Kuma kungiyar ta ce shugaban bai ji dadin abun da ya faru a jahar ba kamar yanda Alwan Hassan ya ce:
”Wallahi Tallahi, Baba Buhari bai ji dadin abun da ya faru a Kano ba, kuma ba ya tare da abun da ya faru a Kano. Babu ruwan shugaban kasa a wannan harkar.”
‘Yan wannan kungiya sun kuma kawar da zargin cewa wai ko suna yi ma jam’iyyar tasu ta APC zagon-kasa ne.

Suka ce, Shugaba Buhari shi ne jagora a jam’iyyar kuma tun da farko ya ce, su je su zabi dan takarar gwamna a kowace jaha, wanda sunka san zai yi abu na adalci.

A dangane da fargabar jam’iyyarsu ta iya rasa kujerar gwamnan jahar Kanon idan aka yi bincike, Mallam Alwan ya ce: ”Duk abun da talaka ya zaba ya ce a ba shi, a ba shi. Mi ya sa?

Bauchi mutuwa sunka yi da gwamnonin da sunka fadi, Adamawa yanzu ya mutu?”
Mallam Alwan ya ce babu wata maganar ko sun hada baki da ‘yan hamayya ne ya sa suke bayyana wannan matsayi.

Yayi nuni da hotunan bidiyo da ya ce duniya ta gani, wadanda a ciki aka ga mataimakin gwamnan jahar ta kano da Kwamishinan kananan hukumomi, wadanda ya ce sun fi kusa da gwamna, sun je karfe biyun dare sun yaga sakamakon zabe.

BBChausa.

Abdul Mailahiya Hausa

I am Abdul Mailahiya Hausa by name, Founder and Operator at Bago Technologies. My hobbies are Reading, Travelling and Discovering.

Post a Comment (0)
Previous Post Next Post